Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Imo, Kennedy Ibe, Ya Yi Murabus, An Nada Sabo

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Imo, Kennedy Ibe, Ya Yi Murabus, An Nada Sabo

  • Rahotanni daga jihar Imo sun nuna cewa kakakin majalisar dokokin jihar, Kennedy Ibe, ya yi murabus daga kujerarsa
  • Yace ya yanke ɗaukar matakin ne bayan dogon nazari da neman shawari, tuni dai aka naɗa sabon kakaki yau Litinin
  • Wannan shi ne karo na huɗu da majalisar ta samu sauyin shugaba cikin shekaru uku da suka gabata

Imo - Kakakin majalisar dokokin jihar Imo dake kudu maso gabashin Najeriya, Kennedy Ibe, ya yi murabus daga kan muƙaminsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Honorabul Ibe, ya yi murabus ne a wurin zaman mambobin majalisar na gaggawa da ya gudana a zauren Majalisar yau Litinin, 19 ga watan Satumba, 2022.

Majalisar dokokin jihar Imo.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Imo, Kennedy Ibe, Ya Yi Murabus, An Nada Sabo Hoto: channelstv

A cewarsa, ya yanke matakin yin murabus ne bayan faɗaɗa neman shawarwari daga iyalai da kuma makusantansa na siyasa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Zabi Ranar Gardama Tsakanin Gwamnati Da ASUU

Haka nan Ibe, ya bayyana cewa murabus ɗin da ya yi daga kujerar kakakin majalisa shi ne mafi Alheri ga iyalan jam'iyyarsa All Progressive Congress (APC) a jihar Imo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma jaddada cewa ba zai yi ƙasa a guiwa ba, zai ci gaba da goyon bayan jam'iyyar APC, gwamnatin jiha da majalisa a jihar Imo.

Majalisa ta rantsar da sabon shugaba

A halin yanzu, mamba mai wakiltar mazaɓar Ehime Mbano, Emeka Nduka, ya karɓi shahadar kama aiki a matsayin sabon kakakin majalisar dokoki ta jihar Imo.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin, Amara Iwuanyanwu, da shugaban masu rinjaye, Kanayo Onyemaechi, sun ta ya sabon shugaban murna bayan Sakataren majalisa ya rantsar da shi nan take.

Bayan zaɓen Nduka, Majalisar dokokin jihar Imo ta yi shugabanni huɗu kenan cikin shekara uku, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu ta Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Abokin Harkarsa Shekaru 21 a Gidan Maza

A wani labarin kuma Majalisar Wakilai Za Ta Dawo Zama A Ranar 20 Ga Watan Satumba A Zauren Wucin Gadi

Majalisar wakilai za ta dawo zamanta a ranar 20 ga watan Satumba bayan hutun shekara da ta tafi tsawon watanni biyu.

A wannan karon, majalisar za ta dawo zama ne a zauren wucin gadi sakamakon gyara da ake yi a tsohon zauren nata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel