Hukumar Zabe Ta INEC Ta Sanya Ranar Gudanar da Zabukan Imo, Kogi da Bayelsa

Hukumar Zabe Ta INEC Ta Sanya Ranar Gudanar da Zabukan Imo, Kogi da Bayelsa

  • Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanya ranar da za a yi zaben gwamna a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi
  • Hakazalika, hukumar ta sanya ranakun da ta amince a yi zabukan fidda gwani a jihohin guda uku
  • Ana sa ran yin zabukan 2023 nan da watanni hudu, lamarin da ke sa hukumomi a Najeriya ke ci gaba da shirye-shirye

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanya ranar da za a gudanar da zabukan jiha a Imo, Bayelsa da jihar kogi, rahoton The Nation.

Hukumar ta sanya ranar 11 ga watan Nuwamban 2023 a matsayin ranar da za a yi zaben gwamna a jihohin uku.

Wannan na fitowa ne daga hukumar a tattaunawar mako-mako da take yi a yau Talata 25 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: Buhari ya bani lambar yabo, da ita zan yi kamfen zaben 2023

Hukumar zabe ta INEC ta bayyana lokacin da za a yi zaben jihohi a Bayelsa, Imo da Kogi
Hukumar Zabe Ta INEC Ta Sanya Ranar Gudanar da Zabukan Imo, Kogi da Bayelsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hakazalika, ta sanya ranakun yin zabukan fidda gwani ga jam'iyyu tsakanin 27 ga watan Maris zuwa 17 ga watan Afrilun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauka sa hannun kwamshinan sadarwa da wayar da kan masu kada kuri'u wannan shawari da hukumar ta yanke ya yi daidai da yadda ta tana na buga ranar zabe kwanaki 360 kafin lokacinsa.

Wa'adin gwamnoni masu ci a jihohin uku

A bangare guda, hukumar ta bayyana lokacin da wa'adin mulki zai kare ga gwamnonin dake ci a wannan jihohi da aka bayyana, rahoton Leadership.

A cewar sanarwar:

"Wa'adin mulkin gwamnan jihar Imo zau kare a ranar 14 ga watan Janairun 2024 yayin da na Kogi da Bayelsa za su kare a ranakun 26 da Janairu da 13 ga Fabrairun 2024 bi da bi."

Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na APC a Wata Jiha, Ta Yi Fatali da Wadanda Suka Ci Zabe

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Port Harcourt ta soke zaben fidda gwanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas, rahoton The Sun.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kotun ta zartar da hukuncin ne a jiya Litinin yayin sauraron wata kara da wasu fusatattun mambobin APCn suka shigar a gabanta.

Idan za a tuna, fusatattun mambobin sun yi zargin cewa an ware su a yayin zaben fidda gwanin jam’iyyar inda suka yi zanga-zanga sakatariyarta da ke Port Harcourt.

Asali: Legit.ng

Online view pixel