'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Fada, Sun Kashe Sarki da Fadawansa a Imo

'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Fada, Sun Kashe Sarki da Fadawansa a Imo

  • Wasu miyagun 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun halaka Basarake da Fadawansa a jihar Imo ranar Litinin
  • Rahotanni da aka tattara sun nuna cewa Basarken na jagorantar taro da manyan yankin lokacin da maharan suka kutsa suka buɗe musu wuta
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan Imo yace yanzu haka yana kokarin fitar da sanarwa ne kan abinda ya auku

Imo - Wasu miyagun 'yan bindiga kusan su 10 sun kai hari fadar Basaraken gargajiya a ƙauyen Obudu Agwa, ƙaramar hukumar Oguta ta jihar Imo ranar Litinin.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa bayan sun kutsa cikin Fadar ana tsaka da taro, yan bindigan sun buɗe wa basataken da mutanensa wuta.

Harin yan bindiga.
'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Fada, Sun Kashe Sarki da Fadawansa a Imo Hoto: punchng
Asali: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun halaka Basaraken mai suna, Eze Ignatius Asor, da wasu fadawansa guda biyu.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojin Najeriya Sun Ceto Mutum 3, Sun Kwayoyi Makamai da Babura daga ‘Yan Ta’adda

A yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Imo, Mike Abattam, yace yana shirya fitar da sanarwa ta musamman a hukumance game da kai harin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa shugabannin al'ummar yankin sun haɗu suna tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yankin a fadar Sarkin lokacin da 'yan bindigan suka kutsa.

Wani shaida da abun ya faru a idonsa daga yankin ya yi ikirarin cewa Basaraken da wasu mutane uku basu motsa ba rai ya yi halinsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bayan waɗanda suka mutu a harin, "Wasu da dama sun ji manyan raunuka, wasu an gaggauta kaisu Asibiti don ceto su amma wasu ba zasu tashi ba."

"Ƙauyen nan na cikin tashin hankali kowa na takansa, mutane na kokarin guduwa don tsira da rayuwarsa. Aƙalla mutum 10 ne suka ji raunuka yayin da wasu suka gudu," inji Ganau.

Kara karanta wannan

An Tafka Mummunan Ta'asa Yayin da Sojoji Suka Dakile Kazamin Harin Yan Ta'adda a Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Halaka Matar Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jihar Nasarawa

A wani labarin kun ji cewa yan bindiga sun kashe matar wani tsohon shugaban ƙaramar hukumar a jihar Nasarawa

Bayanai sun ce matar, wacce sanannar yar kasuwa ce na kan hanyarta ta zuwa kasuwar Assakio lokacin maharan suka farmakesu da safiyar Litinin ɗin nan.

Ta mutu ta bar yara biyu da ta haifa, a yanzun an kai gawarta ɗakin aje gawarwaki gabanin yi mafa jana'iza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel