Karin Bayani: Buhari Ya Dira Jihar Imo Don Kaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka

Karin Bayani: Buhari Ya Dira Jihar Imo Don Kaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar manyan ayyuka 3 a jihar Imo wanda Gwamna Hope Uzodinma na jihar yayi
  • Tun daga filin sauka da tashin jiragen sama, maza sanye da fararen kaya da jajayen huluna da mata sanye da kayan gargajiya suka tarbi shugaban kasan
  • An gano cewa, garin bai yi cikar da ake tsammani ba sakamakon dokar zaman gida ta dole da 'yan awaren IPOB suka kallafa a jihar

Imo - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Imo domin kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar har guda uku.

Jirgin saman shugaban kasan ya sauka a filin jiragen sama na Sam Mbakwe karfe 11 na safiyar Talata, jaridar The Nation ta rahoto.

Buhari
Da Duminsa: Buhari Ya Dira Jihar Imo Don Kaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

An tarbesa tun daga filin sauka da tashin jirage inda dubban jama'a sanye da fararen kaya da jajayen huluna suka cika dankam.

Kara karanta wannan

Ruwan dare: Budurwa ta jawo cece-kuce yayin da ta kammala digiri, tace za ta rushe gidansu

Mata sanye da kayan gargajiya sun dinga cashewa a wurin domin nuna murnar zuwan shugaban kasan a bayyane.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kaddamar da titin Owerri zuwa Orlu da sauran manyan ayyuka. Ana tsammanin zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin jihar.

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon titi mai nisan kilomita 36 daga Owerri zuwa Orlu da kuma kashin farko na tagwayen tititunan Owerri zuwa Okigwe, kamar yadda hadiminsa Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Wannan na zuwa ne ana tsaka da dokar zaman gida ta dole wacce 'yan awaren Biafra suka kallafa a yankin saboda yau an fito da shugaban kungiyarsu, Nnamdi Kanu zuwa kotu a garin Abuja, babban birnin kasar.

Punch ta tattaro cewa, babu mutane masu tarin yawa a inda ake kaddamar da ayyukan kamar yadda ake tsammani, wanda majiya tace baya rasa alaka da dokar zaman gida na dole da IPOB ta kallafa.

Kara karanta wannan

Taraba: Dubban jama'a sun yi wa Nyame maraba bayan Buhari yayi masa rangwame

Sai dai, an tsananta tsaro a wurin da jihar baki daya gudun farmakin da za a iya samu.

Sanata Ubah Ya Magantu Kan Yunkurin Halaka shi da 'Yan Bindiga Suka yi

A wani labari na daban, a ranar Litinin, Sanata Ifeanyi Ubah ya tabbatar da mutuwar wasu daga cikin hadimansa da masu tsaron lafiyarsa a yayin farmakin da aka kai wa tawagarsa a ranar Lahadi.

An kai wa tawagar Sanatan farmaki a wurin kasuwar Nkwo Enugwu dake karamar hukumar Njikoka ta jihar Anambra, jaridar P.M News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel