Yan Bindigar Da Suka Yi Garkuwa Da Wani Basaraken Najeriya Sun Nemi A Biya N200m Kudin Fansa

Yan Bindigar Da Suka Yi Garkuwa Da Wani Basaraken Najeriya Sun Nemi A Biya N200m Kudin Fansa

  • Yan bindigar da suka sace Mai martaba Eze Joel Ndenkwo na jihar Imo sun kira yan uwansa a karo na farko
  • Masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya naira miliyan 200 kafin su sako Basaraken na yankin Isiala Umudi da ke jihar
  • Rundunar yan sandan jihar Imo ta bayyana cewa tuni ta kaddamar da bincike cikin lamarin don kamo miyagun

Imo - Masu garkuwa da mutanen da suka sace wani shahararren basarake a jihar Imo, Eze Joel Ndenkwo, sun bukaci a biya naira miliyan 200 kafin su sako shi.

Yan bindigar sun gabatar da wannan bukata ne jim kadan bayan sun sace shi a gaban ofishinsa da ke hanyar Tetlow a Owerri, babban birnin jihar, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma A Najeriya

Yan sanda
Yan Bindigar Da Suka Yi Garkuwa Da Wani Basaraken Najeriya Sun Nemi A Biya N200m Kudin Fansa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wadanda suka yi garkuwa da basaraken na Isiala Umudi sun jefa shi cikin motarsu ta karfin tuwo sannan suka yi gaba da shi.

Wata majiya ta kusa da basaraken ta bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da shin sun kira kuma sun nemi a biya kudin fansa kafin su sake shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa yan bindigar sun kira daya daga cikin kannensa ta wayar basaraken.

Majiyar ta ce:

“Labarin gaskiya ne. Wadanda suka yi garkuwa da Mai Martaba sun kira waya. Sun kira yan uwansa a karo na farko tun bayan sace shi. Sun bukaci yan uwansa su tanadi naira miliyan 200. Sun kira ta wayar hannunsa. Ina shakka kan inda za su samu irin wannan kudin.”

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, CSP Micheal Abattam, ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da bincike, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Ya'yan zamani: Makiyaya sun sare hannun mahaifinsu domin su raba shi da shanunsa

Mutanen Gari Sun Ga Tashin Hankali, An Yi Garkuwa da Wani Basarake a Najeriya

A baya mun ji cewa wasu da ake zargin miyagun ‘yan bindiga ne sun dauke Mai martaba Eze Jewel Ndenkwo wanda Basarake ne a jihar Imo.

Punch tace Basaraken shi ne shugaban manyan kamfanoni irinsu Udekings Nigeria Limited da ake aiki a yankin kudancin Najeriya.

An dauke Eze Ndenkwo ne a gaban wani kamfaninsa da ke babban birnin Owerri, jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel