Allah Ya Yiwa Wani Tsohon Mataimakin Gwamna A Najeriya Rasuwa

Allah Ya Yiwa Wani Tsohon Mataimakin Gwamna A Najeriya Rasuwa

  • Al'ummar Imo na cikin halin juyayi yayin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Ebere Udeagu, ya kwanta dama
  • Udeagu ya rasu ne bayan an garzaya dashi asibiti a safiyar ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba
  • Marigayin wanda ya yi mataimakin gwamna tsakanin 1999 da 2007 ya mutu yana da shekaru 79

Imo - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Ebere Udeagu, ya rasu a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, yana da shekaru 79 a duniya.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Udeagu, wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna tsakanin shekarar 1999 da 2007 ya rasu ne a safiyar Litinin a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Jihar Imo
Allah Ya Yiwa Wani Tsohon Mataimakin Gwamna A Najeriya Rasuwa Hoto: channels tv
Asali: UGC

Gani na karshe da aka yiwa Udeagu a taron jama’a ya kasance a ranar 1 ga watan Oktoban 2022, lokacin bikin zagayowar ranar yancin kai na 62 a Owerri.

Kara karanta wannan

Rikici: An farmaki hadimin Ganduje a Kano, ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka sace wayarsa

Ya yi yar gajeruwar rashin lafiya

Wata majiya tace tsohon mataimakin gwamnan ya yi korafin rashin jin dadin jikinsa a safiyar ranar Lahadi harma ya kasa halartan taron addu’a a coci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kwashe shi zuwa asibiti inda yace ga garinku a safiyar ranar Litinin.

Wani tsohon gwamnan jihar, Ikedi Ohakin, ya bayyana mutuwar Udeagu a matsayin abun takaici.

Daya daga cikin hadiman Ohakin, Emmanuel Chukwu, a cikin wani dan takaitaccen jawabi da ya saki a ranar Litinin, ya bayyana cewa jihar ta rasa daya daga cikin sanannun ‘ya’yanta, rahoton Nigerian Tribune.

Allah Ya Yi Wa Ɗan Majalisar Katsina Rasuwa A Ƙasar Saudiyya

A wani labarin, mun ji cewa dan majalisa mai wakilan karamar hukumar Bakori a majalisar dokokin jihar Katsina, Dr Ibrahim Aminu Kurami, ya rasu a Saudiya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Na Kusa da Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu

Dan majalisar ya tafi kasa mai tsarkin ne domin yin aikin Umrah, Daily Trust ta rahoto.

A cewar wata majiya daga yan uwansa, ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Madina misalin ƙarfe 2 na dare lokacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel