Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kutsa Ofishin Yan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 4

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kutsa Ofishin Yan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 4

  • Yan bindiga suna cigaba da kai wa jami'an tsaro hare-hare musamman a yankin kudancin Najeriya
  • A deren jiya Juma'a wasu yan bindigan sun kai hari hedkwatar yan sandan da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo
  • Maharan sun kashe jami'an yan sanda guda hudu, sannan sun kona motoccin sintiri da kuma motar DPO tare da kashe wani magidanci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Imo - Wasu bata gari sun kai hari hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya da ke Agwa a karamar hukumar Oguta, Jihar Imo a daren ranar Juma'a sun kashe yan sanda hudu, The Punvh ta rahoto.

Maharan sun kuma kone wasu motocci na rundunar har ma da na DPO.

Taswirar Jihar Imo.
Yan Bindiga Sun Kutsa Ofishin Yan Sanda, Sun Kashe Jami'ai 4. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sace Sarki A Najeriya Bayan Sun Harbi Direbansa

Kuma yan bindigan sun kutsa gidan wani mutum mai suna Ejike sun bindige shi tare da matarsa har lahira.

Hakan ya janyo tashin hankali a unguwar a yayin da yan asalin garin da mazauna suka nuna damuwa matuka.

Majiyoyi wadanda ba su so a ambaci sunansu sun bayyana cewa maharan sun taho ne misalin karfe 10 zuwa 11 na dare a motocci uku.

A cewar majiyoyin, yan bindigan sun taho ne cikin tipper daya da wasu motoccin kirar sienna guda biyu suka afka wa ofishin yan sandan.

Cikin yan sandan da aka kashe, biyu maza ne sannan sauran biyun mata kuma an cinna wa gawarsu wuta.

A cewar majiya, daya daga cikin yan sandan da aka kashe sabon ma'aikaci ne, satinsa biyu da fara aiki.

Daya cikin motoccin da aka kona ta DPO ce.

Wata majiya daga rundunar yan sanda ta ce an turo wasu yan sandan daga wani ofishi su tsare wurin yayin da ake jiran zuwan Kwamishinan yan sanda, Muhammad Berde, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

Mai magana da yawun yan sanda na jihar, CSP Mike Abattam bai riga ya ce komai kan lamarin ba domin kirar da aka yi masa ba su shiga ba.

Yan Bindiga Sun Sace Sarki A Najeriya Bayan Sun Harbi Direbansa

A wani rahoton, yan bindiga sun sace mutane hudu ciki har da basarake na Iku Quaters, Oniku na IKu, a Ikare Akoko ta Jihar Ondo, Cif Mukaila Bello, Leadership ta rahoto.

Tare da basaraken, an cewar wata majiya, an kuma sace Mr Adeniran Adeyemo, Mr Bashiru Adekile da Cif Gbafinro.

Channels TV ta rahoto cewa an sace su ne daren ranar Alhamis a Ago Panu na Owo-Ikare Road, a hanyarsu ta zuwa Akure daga Ikare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel