Yaki da ta'addanci a Najeriya
Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da halaka 'yan bindiga a dajikan kananan hukumomin Giwa da Igabi a jihar Kaduna. Hakan ya faru ne cikin makon da ya gabata.
Jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya DSS sun kai samame gidan wani ɗan adaidaita da ake kyautata zaton yana da alaƙa da ƴan ta'adda a Minna, jihar Neja.
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato sun nuna cewa ƴan bindiga sun hallaka mataimakin kwamandan rundunar sojin Operation Save Haven.
Shugaban jami'ar Dutsin-ma a jihar Katsina (FUDMA), Farfesa Armaya'u Bichi ya zargi wasu ma'aikatan jami'ar da aiki da 'yan ta'adda ta hanyar ba su bayanai.
Shugaban sojin ruwan Najeriya ya ce maganin matsalar tsaro a Najeriya ba komai bane face 'yan Najeriya su koma ga Allah su dukufa da addu'a gadan-gadan.
Shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta Enugu, Farfesa Aloysius Michaels ya gano abin da ya fi kashe 'yan Najeriya tsakanin 'yan ta'adda da rashin kyawun hanyoyi.
Sanata mai wakiltar Ondo ta kudu, Jimoh Ibrahim, ya ce yana da manhaja a wayarsa da ke gano adadin bindigogin da ke cikin zauren majalisar dattawa a kullum.
'Yan sanda a jihar Binuwai sun kama wasu matasa da ake zargi da kone-kone yayin zanga-zanga da aka gudanar ranar Laraba a jihar, kuma zuwa yanzu an kama mutane 18.
A safiyar yau ne 'yan ta'adda su ka kai hari garin Ayati a karamar hukumar Ukum inda su ka kashe mutane 11 ba haira ba dalili, wannan ja jawo mutane yin zanga-zanga.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari