'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Bayin Allah, Sun Kashe Mutane Tare da Tafka Ta'asa Mai Ban Tausayi

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Bayin Allah, Sun Kashe Mutane Tare da Tafka Ta'asa Mai Ban Tausayi

  • Yan bindiga sun kashe bayin Allah har mutum shida yayin da suka kai farmaki kauyuk 3 a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharan sun aikata wannan ta'asa jiya Litinin kuma sun yi awon gaba da mutane masu yawa
  • Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce CP ya tura ƙarin jami'an ƴan sanda zuwa yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki ƙauyukan yankin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga sun afka kauyuka uku daban-daban a ƙaramar hukumar Faskari kuma sun aikata mummunar ta'asa kan bayin Allah.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun toshe fitaccen titi a Arewacin Najeriya, sun sace matafiya masu ɗumbin Yawa

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda.
Yan bindiga sun shiga wani gari a Katsina, Sun Kashe mutane sun kwashi wasu Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph.D
Asali: Facebook

Kamar yadda Channels tv ta tattaro, ƴan ta'addan sun kutsa kai cikin ƙauyen Ƴar Nasarawa, inda suka yi ajalin mutane shida da daren ranar Litinin da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴar Nasarawa dai ya haɗa iyaka da jihar Zamfara kuma yana da nisan kimanin kilomita biyar tsakaninsa da garin Faskari, hedkwatar ƙaramar hukumar Faskari a Katsina.

Haka nan kuma ƙauyen yana kusa da sansanin rundunar sojin Najeriya wanda Birgediya Janar Tukur Yusuf Buratai ya kafa da nufin dawo da zaman lafiya a Arewa maso Yamma da jihar Neja.

Mummunar ɓarnar da ƴan bindiga suka yi

Wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa jaridar Punch ta wayar salula yau Talata cewa ƴan bindiga sun halaka mutum shida a kauyen Ƴar Nasarawa kaɗai kana suka ƙona motoci 8.

Ya ce:

"A kauyen ‘Yar Nasarawa kadai an kashe mutane shida tare da kona motoci takwas. Yanzu haka an yi jana’izar daya daga cikin wadanda suka mutu da safiyar yau (Talata) kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."

Kara karanta wannan

Kwamandojin ƴan ta'adda 3 da wasu mayaƙa 22 sun baƙunci lahira a Borno

An kuma tattaro cewa ƴan bindigan sun sace mutane masu yawa da har yanzu ba a iya tantance adadinsu ba tare da jikkata wasu da dama.

Bayan haka kuma maharan sun ƙona shaguna shida ciki harda ɗakunan ajiyar hatsi da babura waɗanda suke mallakin mazauna kauyen ne.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka a Katsina?

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutane 6 ne suka mutu yayin da wasu akalla 10 suka ji raunuka sakamakon harin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan, Abubakar Aliyu ya fitar, ya ce ‘yan bindigar masu yawa dauke da muggan makamai irin su AK-47 ne suka kai hari kauyen.

Ya ce kwamishinan ƴan sanda, CP Aliyu Musa, ya tura dakaru na musamman da nufin damƙo ƴan bindigan domin su girbi abinda suka aikata.

Wani mazaunin yankin Faskari a Katsina mai suna, Abubakar Awwal, ya shaida wa Legit Hausa cewa maharan sun sace adadin mutum 38 ne a harin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka bayin Allah da yawa a garuruwa 5 a jihar Arewa

Ya faɗa mana cewa ƴan bindigan sun shiga garin Ƴar Nasarawa da ke Gabashin Faskari da daren ranar Litinin, inda suka kashe rayuka 6 ciki harda mai Anguwa kuma suka jikkata 10.

Ya ce:

"Da safiyar nan aka yi jana'izar waɗanda suka rasu a harin. A jiya kaɗai, sun kashe mutum 6 ciki harda mai Anguwa, sun raunata 10, kuma sun yi awon gaba da wasu mutum 38.
"Bayan haka sun ƙona motoci takwas tare da shaguna 10 da gidaje 6, sun aikata ta'addanci mai muni a harin nan, Allah dai ya kawo mana ɗauki."

Jirgin NAF ya ragargaji kwamandojin ISWAP

A wani rahoton kuma Jirgin rundunar sojin sama NAF ya halaka manyan kwamandojin ISWAP uku da ƙarin wasu ƴan ta'adda a wani luguden wuta a jihar Borno.

Zagazola Makama ya tattaro cewa jirgin yaƙin ya yi ruwan bama-bamai kan maɓoyar ƴan ta'addan a kauyen Arinna Woje da ke yankin Marte.

Asali: Legit.ng

Online view pixel