Kwamandojin Ƴan Ta'adda 3 Da Wasu Mayaƙa 22 Sun Baƙunci Lahira a Borno

Kwamandojin Ƴan Ta'adda 3 Da Wasu Mayaƙa 22 Sun Baƙunci Lahira a Borno

  • Jirgin rundunar sojin sama NAF ya halaka manyan kwamandojin ISWAP uku da ƙarin wasu ƴan ta'adda a wani luguden wuta a jihar Borno
  • Zagazola Makama ya tattaro cewa jirgin yaƙin ya yi ruwan bama-bamai kan maɓoyar ƴan ta'addan a kauyen Arinna Woje da ke yankin Marte
  • Wata majiya ta ce tuni aka kwaso gawarwakin ƴan ta'addan kuma aka binne su, inda wasu mambobin ISWAP suka halarci wurin ranar Litinin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Manyan kwamandojin ƙungiyar ƴan ta'adda ISWAP guda uku sun baƙunci lahira yayin da dakarun sojin saman Najeriya suka musu luguden wuta a jihar Borno.

Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan ayyuka ƴan tada ƙayar baya a yankin tafkin Chadi ne ya bayyana haka a shafinsa na manhajar X watau Twitter.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta dauki sabon mataki kan rumbunan masu boye abinci da aka rufe

Dakarun soji sun halaka kwamandojin ISWAP uku.
Kwamandojin ISWAP 3 sun bakunci lahi%a yayin da NAF ta yi musu ruwan wuta a Borno Hoto: Nigeria Air Force HQ
Asali: Facebook

Ya ƙara da cewa luguden wutan jirgin sojin saman ya kuma halaka ƙarin wasu ƴan ta'adda 22.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makama ya yi bayanin cewa sojojin sun samu wannan nasara ne a samamen da suka kai kan ƴan ta'addan a kauyen Arinna Woje, ƙaramar hukumar Marte ranar Lahadi.

Waɗanne kwamandoji ne sojoji suka kashe?

Wata majiya ta shaida wa Makama cewa dakarun sojin sama na rundunar Operation Hadin Kai ne suka yi ruwan bama-bamai a mafakar ƴan ta'addan.

Majiyar ta bayyana sunayen kwamandoji ukun da sojoji suka kashe da suka haɗa da Abacha, Bakura, da kuma Babangida, dan asalin yankin Jibularam a Borno.

Bayanai sun nuna cewa an kwaso gawarwakin ƴan ta'addan kuma an binne su ranar Litinin, inda wasu mambobin ISWAP suka halarci wurin jana'izar.

Wadanda suka halarci wurin binnewar sun hada da Amirul fiye da Abu Hamza da Khaid na Tumbumma da Abu Nazir da Abu Rijal da Khaid na Koloram da sauransu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan bayin Allah, sun kashe mutane tare da tafka ta'asa mai ban tausayi

A ƴan kwanakin nan, dakarun Operation Hadin Kai sun kashe mayakan ISWAP 11 tare da lalata sansanoni 25 na ‘yan ta’adda a dajin Sambisa da Timbuktu Triangle a Borno.

An rasa rayukan mutum 10 a Benuwai

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga da ake zaton miyagun fulani makiyaya ne sun kashe mutum 10 a kauyuka 5 da ke ƙaramar hukumar Apa a jihar Benuwai.

Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun farmaki kauyukan lokaci guda kwanaki uku bayan abinda ya auku a Imana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel