Yan Sanda Sun Kama Dillalin Kwaya Dan Shekara 67 a Legas

Yan Sanda Sun Kama Dillalin Kwaya Dan Shekara 67 a Legas

  • Rundunar 'yan sanda na Sabo da ke jihar Legas ta kama wani dattijo dan shekara 67 yana sayar wa wani dan shekara 22 kwaya
  • An kama dattijon ne a wani sumame da jami'an rundunar suka kai yankin Yaba, kamar yadda rundunar ta sanar a ranar Laraba
  • Wannan sumame ya kara bankado yadda birnin ke yaki da tu'ammali da miyagun kwayoyi a manyan titunan jihar Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - A cikin manyan titunan Legas, inda aikata laifuka ya zama ruwan dare, wani sumamen ‘yan sanda na baya-bayan nan ya bankado yadda birnin ke yaki da tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Wani dattijo mai shekaru 67, Orji Isaac, ya tsinci kansa a hannun 'yan sanda tare da wani matashi mai shekaru 22, Lekan Ganiyu bisa laifin saye da da sayar da muggan kwayoyi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan bindiga a Arewa, sun kwato muggan makamai

Yan sanda sun kama dillalin kwaya dan shekara 67 a Legas
Yan sanda sun kama dillalin kwaya dan shekara 67 a Legas tare da dan shekara 22. Hoto: @LagosPoliceNG
Asali: Twitter

An yi mamakin kama dattijon yana dillacin kwaya

Jami'an rundunar 'yan sanda na Sabo, sun kai sumame a unguwar Yaba, inda suka kama dattijon yana kokarin sayar da kwaya ga matashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da kowa ke kokarin neman ta kansa bayan hango jami'an, an kama Orji Isaac dauke da tarin kwayoyi yana sayarwa.

Kama Isaac ya nuna yadda tu'ammali da muggan kwayoyi ya zama ruwan dare, kuma masu safarar kwayoyin na iya zama babba ko yaro, har ma da dattijai.

Yaki da miyagun kwayoyi a Legas

Rundunar ta tabbatar da kamen ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X @LagosPoliceNG a ranar Laraba.

“Jami’an ‘yan sanda reshen Sabo, a yayin da suke sintiri na sa ido, sun kama wani dillalin miyagun kwayoyi, Isaac, a lokacin da yake sayar wa Ganiyu kwayoyi.

Kara karanta wannan

An karrama wasu jami'an 'yan sanda 4 a kan wata babbar bajinta da suka yi a jihar Arewa

"Za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu idan aka kammala bincike."

- A cewar sanarwa.

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su karacewa ‘tu'ammali da miyagun kwayoyi’.

An karrama jami'an 'yan sanda a jihar Taraba

A wani labarin, kwamishinan 'yan sanda na jihar Taraba, David Iloyalonomo ya karrama wasu jami'an rundunar guda hudu bisa nuna gaskiya da rikon amana.

Legit Hausa ta ruwaito cewa an karrama jami'an ne saboda sun ki karbar cin hancin naira miliyan 8.5 da wani mai garkuwa da mutane ya basu a lokacin da suka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel