Zamfara: Mutuwar Mutum a Hannun Jami'an Tsaro Ya Jawo An Nemi Gwamna Ya Tashi Tsaye

Zamfara: Mutuwar Mutum a Hannun Jami'an Tsaro Ya Jawo An Nemi Gwamna Ya Tashi Tsaye

  • Gwamnatin Dauda Lawal ta kirkiro rundunar Askarawa wadanda suke kokarin yaki da miyagun ‘yan bindiga a jihar Zamfara
  • Ana zargin cewa irin wadannan jami’an sa-kai suna kashe mutanen gari da ba su aikata laifi ba a maimakon su cafke masu barna
  • Abin bai tsaya nan ba, wata rubutacciyar wasika da aka aikawa gwamna ta ce ana zargin siyasa ta shiga aikin wadannan dakaru

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara - Kwanan nan gwamnatin Zamfara a karkashin Dauda Lawal tayi hobbasa wajen magance matsalar rashin tsaro da ke jihar.

Kafin tafiya tayi nisa, an fara zargin Askarawa watau jami’an tsaron sa-kai da aka kafa da hannu wajen mutuwar wani Bawan Allah.

Zamfara
Askarawan jihar Zamfara a Gusau Hoto: Dauda Lawal
Asali: UGC

Aikin Askarawa ya jawo magana

Kara karanta wannan

Murna ta ɓarke yayin da gwamnan APC ya fara siyar da shinkafa kan farashi mai rahusa ga talakawa

Jita-jita tana yawo cewa sabanin siyasa ya shiga tsakanin shugaban rundunar askarawan da wasu fitattun ‘yan siyasa na Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata budaddiyar wasika da Suhailu Mohd ya aikawa gwamnan Zamfara, ya bukaci Mai girma Dauda Lawal ya binciki halin da ake ciki.

Malam Suhailu Mohd wanda ‘dan asalin jihar Zamfara ne kuma mazaunin unguwar Tudun Wadan Gusau ya yabi kokarin gwamna Dauda.

Ana so gwamnatin Zamfara tayi bincike

Amma ya nemi Mai girma gwamna ya binciki yadda Magaji Lawali ya rasu. Tun tuni irinsu Sanata Kabir Garba Marafa suka yi wannan kira.

A wasikar da ya rubuta, wannan bawan Allah ya ce shugaban dakarun Askarawan da mataimakinsa mutanen ‘Yandoto ne a garin Tsafe.

Zamfara: Askarawa sun kashe rai?

Haka zalika wanda ake maganganu game da rasuwarsa shi ma daga kauyen ya fito kuma a 'Yandoto aka birne shi kwanakin bayan nan.

Kara karanta wannan

Akpabio: Karya ake yi, Gwamnati ba ta raba mana N30bn ba - Gwamnonin APC da PDP

A cewar Suhailu, kafin rasuwar Magaji Lawal, ana tuhumar ‘yan sa-kan da tilasta amsa wasu tambayoyi da sunan suna binciken shi.

Marubucin wasikar yake cewa iyalan marigayin sun ga matsin lamba daga Askawara domin su ce yana da alaka da ‘yan bindiga.

Idan abin da yake cikin wasikar sun tabbata, babu jituwa tsakanin Askarawan da wasu manya da ke garuruwan Gusau da na Tsafe.

Tun kafin sunan jami’an sa-kan ya baci, marubucin ya roki gwamna Lawal ya binciki lamarin ta hanyar kafa kwamiti na musamman.

Iyalan mamaci sun yi magana

A wani rahoto, ana da labari cewa zargin kisan da hukumar tsaron CPG ta yi wa Magaji Lawal ya tada jijiyoyin wuya a jihar Zamfara.

Iyalan marigayin sun tabbatar da cewa akwai siyasa a mutuwar har kwamandan hukumar, Kanal Rabi'u Yandoto ya maida martani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel