Ribadu: Bayanai Sun Fito Bayan Kus-Kus da Hadimin Tinubu Yayi da Sanatoci a Majalisa

Ribadu: Bayanai Sun Fito Bayan Kus-Kus da Hadimin Tinubu Yayi da Sanatoci a Majalisa

  • Nuhu Ribadu ya gana da sanatoci a majalisar dattawa kuma ya gabatar masu da bayanin halin da ake ciki a bangaren tsaro
  • Alkaluman Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro sun nuna ana samun saukin ‘yan ta’adda da 'yan bindiga
  • Malam Ribadu ya fadawa ‘yan majalisa kokarin da aka yi wajen yakar Boko Haram, IPOB da ‘yan bindiga a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya yi zaman sirri da Sanatocin Najeriya a ranar Talatar nan.

Premium Times ta bi diddiki domin gano yadda muhimmin zama ya kasance. Hafsoshin tsaro sun je majalisar kuma sun yi magana.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya samu babban mukami, kungiyar AU ta ba shi nauyi a nahiyar Afrika

Nuhu Ribadu
Nuhu Ribadu ya ce rashin tsaro ya ragu Hoto: @NuhuRibadu/@NDefenceAcademy
Asali: Twitter

Ministocin tarayya kamar Olubunmi Tunji-Ojo, Wale Edun da Ibrahim Geidam suna cikin wadanda aka sa labule da su a majalisar dattawan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin Nuhu Ribadu a kan Boko Haram

Nuhu Ribadu ya yi bayani a game da ta’addanci da kungiyoyin da ke tada kayar baya, ya kuma fadi yadda su ke kokarin magance matsalar.

A cikin watanni shida da suka gabata, Nuhu Ribadu ya ce hare-haren ‘yan Boko Haram a Arewa maso gabas ya ragu sosai zuwa 8%.

A shekarar da ta gabata, Ribadu ya ce ‘yan ta’addan sun kai hare-hare 394, daga ciki 64 (16.24%) kadai aka samu a mulkin Bola Tinubu.

Sakamakon kokarin da aka yi, ‘yan ta’addan sun komawa kai harin sunkuru da dasa bam. 78% na artabun, sojoji ke kai wa miyagun hari.

Ribadu ya yabawa gwamnatin Babagana Zulum wajen karya ta’addancin ‘yan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Muhimman matakai 6 da aka dauka da Tinubu ya zauna da Gwamnoni a Aso Villa

An samu saukin IPOB inji Ribadu

Mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaron ya yi bayani game da yadda aka bi domin takaita hare-haren ‘yan ta’addan IPOB a kasar.

Daga lokacin da Ribadu ya shiga ofis, barnar IPOB ta ragu da 75% a kudu maso gabas. Kafin nan kuwa sun rusa ofishin ‘yan sanda 164.

Ta’adin ‘yan bindiga ya ragu da 45% a bara a bayanin da jaridar ta ce Ribadu ya yi. An kuma yi nasarar ceto mutane fiye da 700 a yankin.

Bayanin da NSA ya gabatar ya kunshi yadda jami’an tsaro suka gano makamai sama da 5000 kuma aka kara adadin man da ake hakowa.

Daga cikin dalilan da ke jawo matsalar tsaro kamar yadda aka fahimta akwai rashin aikin yi da dole gwamnati ta dage wajen rage shi.

Tinubu ya zauna da Gwamnoni

Gwamnatin Kano tana yakar masu boye kayan abinci duk da wasu sun soki matakin da aka dauka, an ji labari Bola Tinubu ya ji dadin hakan.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilci gwamnan Kano watau Abba Kabir Yusuf da aka yi zama a kan halin tsadar rayuwa a fadar Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel