Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Tarwatsa Mutanen Garuruwa 10 a Jihar Arewa, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Tarwatsa Mutanen Garuruwa 10 a Jihar Arewa, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

  • Ƴan bindigan daji sun raba mutanen kauyuka aƙalla 10 daga gidajensu da gonakin su a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna
  • Wani shugaban al'umma a ɗaya daga cikin ƙauyukan, Malam Jafaru Anguwar Salahu, ya ce yanzu sun koma ƴan gudun hijira a wasu yankunan
  • Ya yi kira ga gwammati ta kawo.musu agaji ta hanyar tsaftace kauyukan daga ta'addancin ƴan bindiga domin su koma gidajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Miyagun ƴan bindiga sun tarwatsa mutanen kauyuka alal aƙalla 10 a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, mazauna garuruwan sun tarwatse sun bar gidajensu ne saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gano maboyar makamai a jihar Arewa, sun cafke wadanda ake zargi

Gwamna Malam Uba Sani ns jihar Kaduna.
Yan Bindiga Sun Tarwatsa Kauyuka 10 a Jihar Kaduna, Sun Tafka Ta'adi Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Mafi akasarin mutanen waɗannan kauyukan sun gudu zuwa garuruwan da suka fi tsaro da ke maƙotaka da su a yankin Igabi yayin da wasu kuma suka koma Zaria.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani shugaban al'umma a ɗaya daga cikin kauyukan da abun ya shafa, Malam Jafaru Anguwar Salahu, ya ce mafi yawan mazauna kauyukan sun zama ƴan gudun hijira a wasu wuraren.

Wane kauyuka ƴan bindiga suka kori mutane?

Ya lissafa kauyukan da aka tarwatsa mutanen su da suka hada da Sabon Gida, Anaba, Anguwar Salahu, Guberawa, Garu, Rafin Iwa, Gidanduki, Anguwan Najaja, Kunza, da Anguwan Magaji.

"Duk wadannan kauyukan da na ambata a da akwai mutane, amma yanzu duk an raba mu da gidajenmu da gonakinmu."
"Yanzu da nake magana da ku, mun zama ƴan gudun hijira a yankin gundumar Gwada da wasu ƙauyuka."
"Muna rayuwa ne kawai amma bamu san me zamu yi ba kwata-kwata," in ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka shugaban al'umma a wani sabon hari

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta taimaka ta kawo musu ɗauki ta hanyar tsaftace garuruwansu daga ayyukan ƴan bindigan daji da dawo da zaman lafiya.

A cewarsa, ta haka ne kaɗai za su samu damar komawa gida su ci gaba da harkokinsu da sana'ar su ta noma.

Yan sanda sun ceto fasinjoji 16

A wani rahoton kuma Ƴan sanda da sojoji sun ceto matafiya 16 da ƴan bindiga suka sace daga motoci biyu a jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP William Aya, ya ce jami'an tsaron sun kai ɗauki bayan samun rahoton sace fasinjojin jiya Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel