Zaben Najeriya
Kotun Daukaka Kara ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Kogi da Murtala Ajaka na SDP ke kalubalantar Gwamna Usman Ododo na jam'iyyar APC.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sha alwashin hana sanatar Abuja, Ireti Kingibe dawowa Majalisar Dattawa a Najeriya kan kalamanta game da jagorancinsa a birnin.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta a jihar Rivers (RSIEC) ta sanya ranar da za ta gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi 23 da ake fadin jihar.
Kungiyar matasan Arewa ta AYCF ta zargi ziyarar Rabiu Kwankwaso ga Nasir El-Rufai a matsayin kulle-kullen siyasa saboda zaben 2027 domin kifar da Bola Tinubu.
Kamfanin jaridar This Nigeria ya zabi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a matsayin gwarzon gwamna na shekarar 2024. An zabe shi ne saboda jarumta da ya nuna.
Majalisar dattawan Najeriya ta yanke hutun babbar sallah da ta dauka domin tattauna manyan abubuwan da suka shafi tsarin kasa da lamuran zabe a yau Alhamis.
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Bishof Isaac Idahosa ya yaba da yadda ya mutane ke son jagoran kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Tsohon kakakin majalisar wakilar Yakuba Dogara ya bayyana babban kalubalen da tsarin mulkin farar hular ke fuskanta, wanda ya danganta da talauci.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi haɗin kan jam'iyyun siyasa domin ceto Najeriya daga ƙangin da mulkin APC ya jefa ta a ciki.
Zaben Najeriya
Samu kari