Kungiyar CAN Tayi Wani Muhimmin Kira Ga Masu Kada Kuri'a a Kaduna

Kungiyar CAN Tayi Wani Muhimmin Kira Ga Masu Kada Kuri'a a Kaduna

  • Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) tayi kira ga al'umma da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatar su domin kaɗa ƙuri'a ranar zaɓe
  • Ƙungiyar tayi kira ga hukumar INEC da ta zauna a tsakiya kada ta nuna fifiko kan wata jam'iyya a zaɓen
  • Shugaban ƙungiyar na jihar ya kuma buƙaci jami'an tsaro da su tabbatar mutane sun samun ƴancin sauke nauyin dake kan su ba tare da wani tsoro ba

Jihar Kaduna- Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) da kwamitin zaman lafiya na jihar Kaduna (KSPMWC), sun yi kira ga masu kaɗa ƙuri'u da kada su yi sanyi su tabbatar sun fito ƙwan su da ƙwarƙwatar su sun zaɓi ƴan takarar da suke so a zaɓen gwamna da na majalisar dokoki na ranar Asabar.

Shugaban ƙungiyar reshen jihar Kaduna, Rev. Joseph Hayab, shine ya bayar da wannan shawarar a ranar Alhamis, 16 ga watan Maris 2023. Rahoton The Guardian

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Kaduna, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Zazzafan Umurni

Hayab
Kungiyar CAN Tayi Wani Muhimmin Kira Ga Masu Kada Kuri'a a Kaduna Hoto: The Guardian
Asali: UGC

A kalamansa:

“CAN tana neman hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta tsaya tsaki domin dawo da martaɓar ƙimarta da ta zube a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata a dalilin rashin gaskiyar ta."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Dole ne hukumar INEC ta tabbatar tayi aiki da umurnin sabuwar dokar zaɓe."
“Haka kuma, CAN tana roƙon jami'an tsaro da su nuna ƙwarewa ta hanyar tabbatar da cewa mutane sun kaɗa ƙuri'un su cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro, tsangwama ko fargaba ba."

Hayab ya kuma yi bayanin cewa ƙungiyar CAN na kira ga al'umma da su kiyayi yin kalaman tunzura domin daga ƙarshe dai mutum ɗaya ne kawai zai samu nasara. Rahoton The Street Journal

Ya kuma buƙaci ƴan takara da su rungumi juna domin gina jihar da za suyi alfahari da ita gabanin zaɓe, lokacin zaɓe da bayan kammala zaɓuka.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zabe, Gwamna El-Rufai Ya Ware Makudan Kudi Zai Biya 'Yan Fansho Da Gratuti

“Mu zaɓi shugabanni waɗanda za su samar da cigaba, kare lafiya, ba kowa dama da ciyar da jihar gaba." Inji shi

Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohi Da APC Za Ta Iya Lallasa PDP Da Sauran Jam'iyyu

A wani labarin na daban kuma, mun kawo muku jerin jihohin da jam'iyyar APC zata iya lallasa PDP da sauran jam'iyyun adawa.

Zaben gwamnonin dake tafe dai za a fafata sosai a tsakanin jam'iyyu a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel