Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohi Da APC Za Ta Iya Lallasa PDP Da Sauran Jam'iyyu

Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohi Da APC Za Ta Iya Lallasa PDP Da Sauran Jam'iyyu

Jam'iyyun siyasa, yan takara, masu ruwa da tsaki da al'ummar kasa na jiran ranar 18 ga watan Maris ta yi domin a yi zabe kowa ya san matsayinsa.

Da farko an yi niyyar yin zabukan gwamnonin jihohi da yan majalisun jiohin ne a ranar 11 ga watan Maris amma hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta daga zaben da kwana 7.

Gwamnonin APC
Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohi Da APC Za Ta Iya Lallasa PDP Da Sauran Jam'iyyu. Hoto: Nigerian Tribune/Premium Times/Leadership
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben ya ce an dage zaben ne don bawa hukumar dama ta sake saita na'urar tantance masu kada kuri'a ta BVAS.

Za a yi fafata zaben gwamnonin ne a jihohi 28 cikin 36 da ke Najeriya.

A bisa hakan Legit.ng Hausa ta jero muku wasu jihohin Najeriya da ake kyautata zaton jam'iyyar All Progressives Party, APC, mai mulki a kasa ne za ta iya lashe su a zaben da aka fatan yi a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnoni: Jihohi 28 ne za a yi zabe gobe Asabar, ga jerin sunayensu

Sakamakon nazari na jin ra'ayoyin yan Najeriya da kungiyoyin Enough is Enough (EiE) da SB Morgen (SBM) suka yi ya nuna cewa jam'iyyar ta APC za ta iya lashe jihohi 10 a zaben da ke tafe.

Jerin Jihohin da ake ganin jam'iyyar APC ce za ta iya yin nasara a zabukan gwamnoni na ranar 18 ga watan Maris.

1. Benue

2. Nasarawa

3. Niger

4. Kwara

5. Ogun

6. Legas

7. Zamfara

8. Jigawa

9. Yobe

10. Borno

"Babu Wanda Na Janye Wa Takara", Asake, Dan Takarar Gwamna Na LP A Kaduna

Jonathan Asake, dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a Jihar Kaduna ya karyata jita-jitar cewa ya janye wa dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Isah Ashiru, takara a zaben ranar Asabar da ta tafe.

Ya bayyana hakan ne yayin wani hira da ta yi da manema labarai a garin Kafanchan, hedikwatar karamar hukumar Jema'a a yayin mayar da martani kan batun.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Tarayya Ta Tsayar Da Sabon Lokacin Kidaya Yan Najeriya

Kazalika, Asake ya zargi shugaban jam'iyyar PDP na Kaduna, Hassan Hyer da neman bata masa suna ta hanyar zarginsa da karkatar da kudi naira miliyan 120 da Gwamnan Ribas Nyesom Wike ya ba wa mutanen Kudancin Kaduna a matsayin tallafi da hannun kungiyar mazauna Kudancin Kaduna (SOKAPU), lokacin yana jagorantar kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel