Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace A Sani Game Da Umar Namadi, Dan Takarar Gwamnan APC a Jigawa

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace A Sani Game Da Umar Namadi, Dan Takarar Gwamnan APC a Jigawa

Masu zabe a Najeriya dai suna cikin shiri suna jiran ranar 18 ga watan Maris domin su fita su jefa kuri'unsu ga yan takarar gwamna da majalisar jiha da suka kauna.

Yan takarar su kuma a bangarensu sun kwashe watanni suna bi lunguna da sakuna suna tallata kansu da ayyukan da za su yi wa al'umma idan an zabe su.

Umar Namadi
Umar Namadi: Wasu Muhimman abubuwa game da dan takarar gwamnan jihar Jigawa. Hoto: Solacebase
Asali: Facebook

Daya daga cikin irin wadannan yan takarar shine Alhaji Umar Namadi wanda aka fi sani da Danmodi, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a Jihar Jigawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba tare da tsawaita jawabi ba, Legit.ng zai kawo wasu bayanai masu muhimmanci dangane da mataimakin gwamnan na jihar Jigawa wanda ke fatan gadon kujerar mai gidansa, Gwamna Muhammad Badaru wanda ya yi wa'adinsa biyu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Kama Yan NNPP 2 Da Ke Shirin Tada Zaune Tsaye Yayin Zaben Gwamna a Kano

1. An haifi Alhaji Umar Namadi (Danmodi) ne a ranar 7 ga watan Afrilun 1963 a garin Kafin Hausa da ke karamar hukumar Kafin Hausa na Jihar Jigawa.

2. Ya yi karatun frimare da sakandare a garin Kafin Hausa sannan ya tafi Jami'ar Bayero ta Kano inda ya yi digirinsa na farko a bangaren akanta (Accountancy) a shekarar 1987.

Ya kuma yi digiri na biyu a bangaren ilimin harkokin kasuwanci wato MBA duk a BUK, ya kammala a 1993.

3. Bayan zama kwararren akanta (Chartered Accountant), ya kafa kamfaninsa na akantanci, Namadi, Umar and Co Chartered Accountants a Kano.

Ya jagoranci sashin akantanci na kamfanin Dangote Group na wasu shekaru, shi mamba ne na kungiyoyin manyan akantoci kamar NIM, ICAN, CITN.

4. Ya yi aiki a matsayin kwamishinan kudi har zuwa 2019. Ya taba rike mukamin shugaban kungiyar kananan masana'antu (NASI).

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

5. Namadi ya yi ayyukan bincike a kan Madogarawa da Aiwatar da Kudade, Binciken Tsarin Bayanai na Na’ura mai kwakwalwa da Bankin Al’umma

6. Danmodi ya shiga siyasa ne karara a shekarar 2019, lokacin da Gwamna Badaru ya dauke shi a matsayin mataimakin gwamna ya maye gurbin Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin gwamna.

Daga bisani ya kuma yi takarar neman tikitin gwamna a 2023 inda ya samu nasara da kuri'u 1,220.

7. Umar Namadi yana da aure da yara amma bincike bai tabbatar da adadinsu ba.

Nasiru Yusuf Gawuna: Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

Dr Nasiru Yusuf Gawuna shine mataimakin gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam'iyyar APC da ke fatan darewa kan kujerar mai gidansa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Gawuna ya taba rike mukamin kwamishinan noma na jihar Kano kuma ya yi aiki da gwamnatoci uku a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel