Alhaji Aminu Dantata Ya Musanta Goyon Bayan Dan Takarar Ganduje

Alhaji Aminu Dantata Ya Musanta Goyon Bayan Dan Takarar Ganduje

  • Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya fito ya musanta raɗe-raɗen da akw yaɗawa kan cewa yace a zaɓi ɗan takarar gwamnan APC a Kano
  • Wasu rahotannin kanzon kurege dai sun yi ta yawo a jihar Kano inda suke cewa dattijon yace a zaɓi Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC
  • Sai dai, Dattijon ya musanta hakan inda yace shi uba ne ga kowa kuma baya goyon bayan wata jam'iyya ko wani ɗan takara

Jihar Kano- Babban ɗan kasuwa kuma dattijon ƙasa, Alhaji Aminu Dantata, ya musanta rahotannin da ake yaɗawa cewa ya nuna goyon bayan sa ga Nasiru Gawuna, ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Rahotanni da dama sun yi ta yawo a jihar Kano cewa dattijon ya marawa Gawuna baya a zaɓen gwamnan jihar. Rahotannin dai sun fara yawo ne a cikin farkon satin nan. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

"Ban Da Jam'iyya Yanzu" Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Ya Gudu Daga PDP Bayan Atiku Ya Faɗi

Dantata
Alhaji Aminu Dantata Ya Musanta Goyon Bayan Dan Takarar Ganduje Hoto: Business Day
Asali: UGC

Da yawa daga cikin waɗanda suke yawo da waɗannan rahotannin suna kafa hujja kan marawa Gawuna baya kan dangantaka mai tsami dake a tsakanin Alhaji Aminu Dantata da jagoran jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, babbar jam'iyyar adawa a jihar.

Sai dai, Alhaji Dantata, ta hannun sakataren sa na musamman, Mustapha Abdullahi Junaid, ya bayyana cewa ba ruwan shi da tsoma baki cikin harkokin siyasa. Mustapha ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya fitar a shafin sa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mustapha Junaid ya bayyana cewa Dantata bai taɓa marawa wata jam'iyya ko wani ɗan takara baya ba, sannan zai cigaba da zama ɗan ba ruwan mu kamar yadda ya saba a lokutan zaɓe.

Sanarwar na cewa:

"Ina sanar da mutane cewa Aminu Alhassan Dantata bai ce a zabi Gawuna ba, kuma bai ce a zabi kowa ba, domin shi Uba ne a wajan kowa, saboda haka masu yada wannan jita-jita su daina kuma suyi gaggawa wajan cire rubutun da suka yi. Mungode."

Kara karanta wannan

Kwana 7 Gabanin Zaben Gwamna, Jam'iyya Ta Dakatar Da Shugabanta Na Jihar Kaduna

Jamilu Gwamna Ya Karyata Batun Yi Wa Al’ummar Gombe Barazana Da Mutuwa

A wani labarin na daban kuma, jigo a jam'iyyar APC ya jihar Gombe, ya musanta batun da ake yaɗawa cewa yaa yiwa al'ummar jihar barazanar kisa.

Jamilu Isyaku Gwamna ya ƙaryata wannan zargin da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel