Zaben 2023: Cikin Mako Daya An Turo Kwamishinonin 'Yan Sanda 5 Jihar Kano

Zaben 2023: Cikin Mako Daya An Turo Kwamishinonin 'Yan Sanda 5 Jihar Kano

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya a cikin kwana bakwai ta tura kwamishinonin ƴan sanda biyar jihar Kano
  • Wannan sauye-sauyen na sababbin kwamishinonin ƴan sandan ya janyo cece-kuce a jihar ta Kano
  • Sai dai mataimakin sufeto janar na ƴan sanda yayi ƙarin haske kan dalilin da ya sanya aka samu wannan sauye-sauyen a jihar da ma wasu jihohi a ƙasar nan

Jihar Kano- Hukumomin ƴan sandan Najeriya sun tura tare da sauyawa kwamishinonin ƴan sanda biyar jihar Kano a cikin mako ɗaya. Rahoton Daily Trust

Hakan na zuwa ne bayan yadda abubuwa suka ɗauki zafi a jihar a yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna dana ƴan majalisar dokojin jihar na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Usman Baba
Zaben 2023: Cikin Mako Daya An Turo Kwamishinonin 'Yan Sanda 5 Jihar Kano Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A ranar 21 ga watan Fabrairu, IGP Usman Baba Alkali ya tura CP Muhammad Yakubu jihar Kano domin karɓar ragamar rundunar ƴan sanda jihar daga hannun CP Mamman Dauda, wanda aka tura zuwa jihar Plateau. Rahoton The Guardian

Kara karanta wannan

"Har Yanzu Kwankwaso Amini Na Ne" Gwamna Ganduje Ya Bayyana Dangantakarsa Da Kwankwaso

Bayan Yakubu an turo CP Balarabe Sule wanda tsohon shugaban masu tsaron Ganduje ne. Sai dai an soke dawo da shi Kano a ranar 8 ga watan Maris bayan an gudanar da zanga-zanga a jihar ta nuna ƙin amincewa da hakan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga nan sai aka turo CP Faleye Olaleye zuwa jihar amma an sauya shi da CP Ahmed Kontagora domin jagorantar rundunar a lokacin zaɓe.

Rahoto ya nuna cewa a ranar Talata aka soke turo Kontagora zuwa Kano inda aka sauya shi da CP Usaini Gumel.

Mataimakin sufeto janar na ƴan sanda (DIG) mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma kan harkokin zaɓe, Hafiz Inuwa, yayi bayani kan wannan sauye-sauyen kwamishinonin da aka samu a jihar biyon bayan cece-kucen da suka janyo.

Da yake magana da ƴan jarida a ranar Laraba a Kano, DIG Inuwa ya bayyana cewa ba a jihar Kano kaɗai ake yin irin hakan ba.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Sheke Wani Dan Ta'adda Da Fatattakar Da Dama Daga Cikin Su

"An yi sauye-sauyen ne domin muna so mu nuna cewa ƴan sanda ba ruwan su da siyasa. Muna so mu ba kowa mamaki." Inji shi

Ya kuma cigaba da bayanin anyi sauye-sauyen ne domin tabbatar da cewa:

“Babu wanda ya isa ya juya akalar rundunar ƴan sandan Najeriya. Abinda yake cikin ran sufeto janar shine zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma yin sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali. Wannan shine dalilin da ya sanya akayi sauye-sauyen a faɗin ƙasar nan."

Jam'iyyar NNPP a Kano Ta Zargi Hukumar DSS Da Hada Baki Da APC

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar NNPP ta zargi hukumar DSS da haɗa baki da jam'iyyar APC a jihar.

Jam'iyar NNPP tace akwai wata ƙullalliya da hukumar ke shirya mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel