Garba Shehu Yayi Magana Kan Zaben Shugaban Ƙasa Da Aka Gudanar

Garba Shehu Yayi Magana Kan Zaben Shugaban Ƙasa Da Aka Gudanar

  • Babban hadimin shugaba Buhari ya bayyana cewa sumul ƙalau aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya
  • Garba Shehu yayi nuni da cewa ƴan Najeriya sun gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana
  • Yace zaɓen shugaban ƙasan wani babban cigaba ne kan sauran zaɓukan da aka taɓa gudanarwa a ƙasar nan

Abuja- Babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan watsa labarai, Garba Shehu, ya bayyana cewa kaso 98 ko 99 na ƴan Najeriya suka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu cikin kwanciyar hankali.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin da tattauna da gidan talabijin na Arise Tv a shirin su na 'The Morning Show' ranar Alhamis. Rahoton Vanguard

Shehu
Garba Shehu Yayi Magana Kan Zaben Shugaban Ƙasa Da Aka Gudanar Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasan, kuskure ne babba ace an samu tashin hankali a zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Daga Ƙarshe Peter Obi Ya Bayyana Takamaiman Dalilin Sa Na Garzayawa Kotu Kan Zaɓen Tinubu

Idan za a iya tunawa dai an samu rahotannin ɓarkewar rikici lokacin zaɓen shugaban ƙasa a jihohin Katsina, Legas, Delta da Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiyar Plateau, ƴan daba har farmakar cibiyar tattara sakamakon zaɓen jihar suka yi, inda suka kawo tsaiko wajen bayyana sakamakon zaɓen.

Sai dai, Shehu yace rahotannin rikicin zaɓen ƴan kaɗan ne kawai inda ya ƙara da cewa zaɓen shugaban ƙasar ya ɗararwa sauran zaɓukan da aka taɓa yi a baya a ƙasar. Rahoton The Cable

A kalamansa:

“Maganar rikici, tabbas na ƙalilan daga ciki ban musanta hakan ba."
“Amma ace wannan zaɓen ya zo da rikice-rikice, babu wanda zai iya kare hakan. Eh akwai ƴan kaɗan amma abubuwan da muka gani sun sha bamban dana baya."
“A bisa hakana, nayi amanna cewa ƙasar nan yakamata ta godewa jami'an tsaro saboda sune suke jajirce suka tsaya kai da fata wajen tabbatar da cewa kas 98%, 99% na ƴan Najeriya sun yi zaɓe ba tare tsoro ko kowace irin fargaba ba."

Kara karanta wannan

"Tunda mun ci zabe a baiwa Kirista shugabancin APC": Rikici ya kunno kai a uwar Jam'iyya

Zaben 2023: Cikin Mako Daya An Turo Kwamishinonin 'Yan Sanda 5 Jihar Kano

A wani labarin na daban kuma, ruɗani ya biyo bayan tura kwamishinonin ƴan sanda 5 zuwa jihar Kano a cikin mako ɗaya.

A cikin mako ɗaya dai sufeto janar na ƴan sanda, IGP Usman Baba, ya tura kwamishinonin ƴan sanda 5 zuwa jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel