2023: Jonathan Ya Ba Wa Yan Siyasa Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Daf Da Zaben Gwamnoni

2023: Jonathan Ya Ba Wa Yan Siyasa Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Daf Da Zaben Gwamnoni

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya bukaci yan siyasa da su guji tursasa kan su kan kujerar jagoranci
  • Jonathan ya ce bai kamata mutum ya zubar da jinin al'ummar da ya ke da burin jagoranta da nufin jagoranci ko a mutu ko ayi rai
  • Jonathan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa bisa rashin mahaifinsa

Bayelsa - A shirye shiryen zaben gwamna da na yan majalisar jiha da za a gudanar ranar Asabar, tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya hori yan siyasa da su guji siyasar ko a mutu ko a yi rai, ya na cewa wanda ke son mulki bai kamata su tursasa kansu ga jama'a ba.

Jonathan ya bada shawarar a ranar Alhamis a garin Sampou da ke karamar hukumar Kolokuma/Opokuma a Jihar Bayelsa jim kadan bayan ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamna Douye Diri wanda ya rasa mahaifinsa, Pa Abraham Diri.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Rundunar Yan Sanda Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al’ummar Jihar Kano Ana Gab Da Zabe

Jonathan
Jonathan Ya Ba Wa Yan Siyasa Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Daf Da Zaben Gwamnoni
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa a Bayelsa, jihar tsohon shugaban kasar, za a gudanar da zaben yan majalisar jiha ranar Asabar yayin da za ayi zaben gwamna 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Mai magana da yawun Gwamna Douye Diri, Mr Daniel Alabrah, ya shaidawa manema labarai a wata sanarwa ranar Alhamis cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ya bukaci yan siyasa da su zama masu taimakon al'umma ba kansu ba, ya na rokon yan siyasa da su jira lokacin da Allah ya tsara mu su don hawa kujerar shugabanci.

Jonathan ya bayyana cewa a dimukradiyya, mutane su na taka muhimmiyar rawa kuma yana mamakin yadda wasu ke tilasta kan su don mulkar al'umma.

Ya kuma shawarci al'ummar jihar da su kasance cikin lumana lokacin gudanar da zabe.

''Shugabanci ba dole. Abu ne na bautawa al'umma. To, idan kana son jagorantar al'umma, ba zai yi wu ka kashe su kafin ka jagorance su ba.

Kara karanta wannan

Abinda Ya Sa Na Zubda Hawaye Lokacin da Na Zama Mataimakin Marigayi Yar'adua, Jonathan Ya Magantu

''A Bayelsa, kalubalen zai zo da sauki saboda ba za a yi zaben gwamna ranar Asabar ba. Amma ina rokon mutane da su yi zabe lafiya,'' in ji Jonathan.

Da ya ke magana akan marigayi Pa Diri, tsohon shugaban kasar ya ce mutuwar iyaye akwai ciwo amma ya na rokon iyalan mamacin da su dangana saboda ya bar baya mai kyau.

Ya ce ganin yadda Diri ya samar da gwamna na nufin yadda ya tarbiyantar da 'ya'yansa ya kuma roki Allah ya bawa iyalan Diri hakurin jure rashin.

Ya ce:

''Idan ka je ziyarar ta'aziyya, wani lokacin ka na rasa abin fada. Mun yi sa'a ubanmu ya rayu shekara 88 amma ba shi ne abu mafi muhimmanci ba. Abin da za tuna shi da shi abu mai muhimmanci. Daga sakonnin da aka samu, abu ne a bayyane ya rayu cikin mutunci.
''Ya na da nagartar da watakila ita ta taimake shi ya samar da gwamna. Mun zo don taya gwamna da iyalansa da ragowar mutane jimami da kuma jaje ga sauran iyalansa.''

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

A nasa bangaren, gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana ziyarar tsohon shugaban kasar a matsayin ta musamman, ya na cewa iyalansa da al'umma sun samu kwarin gwiwa saboda ganinsa a wajen.

Ya bayyana irin alakar da ke tsakaninsa da Jonathan lokacin da ya ke (Jonathan) mataimakin gwamnan Bayelsa.

Diri ya ce ya na da alaka mai kyau da Jonathan har sanda ya zama gwamna ya kuma nada shi (Diri) a matsayin Kwamishina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel