"Ina Da Dangantaka Mai Kyau Tsakani Na Da Kwankwaso", Ganduje

"Ina Da Dangantaka Mai Kyau Tsakani Na Da Kwankwaso", Ganduje

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dangantakar dake tsakanin sa da Rabiu Musa Kwankwaso
  • Gwamnan yayi nuni da cewa duk da banbancin ra'ayin siyasa dake a tsakanin su, dantakar su mai kyau ce
  • Ganduje ya kuma yi kira ga jam'iyyun siyasa da su zama masu kira zuwa ga zaman lafiya maimakon yin abubuwan da ka iya tayar da fitina

Jihar Kano- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ƴan siyasa duk irin saɓanin da ƴan siyasa za su samu, tabbas watarana zasu iya komawa inuwa ɗaya.

Gwamnan ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, har yanzu aminin sa ne. Rahoton The Guardian

Ganduje
"Ina Da Dangantaka Mai Kyau Tsakani Na Da Kwankwaso", Ganduje Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Ganduje ya bayyana cewa babu wani abun da yake shiryawa lokacin da aka ga ya tuƙa tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau, zuwa gidan sa suka sanya labule.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

Ganduje ya bayyana hakan ne a wajen wata liyafar cin abinci da aka shirya domin zaman lafiya, wacce kwamitin zaman lafiya na Kano tare da haɗin guiwar kwamitin zaman lafiya na ƙasa suka shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gudanar da liyafar ne domin ƙara ƙarfafa zaman lafiya a yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna da na ƴan majalisun dokokin jihar na ranar Asabar.

Ganduje ya aminta cewa siyasa mugun wasa ne sannan ya shawarci masu ruwa da tsaki da jam'iyyun siyasa su tabbatar suna kira zuwa ga zaman lafiya da ƙulla dangantaka mai kyau da zaɓe ba tare da fitina ba.

Ya bayyana cewa lokaci yayi da yakamata jam'iyyun siyasa su mayar da hankali wajen yin kamfen kan abubuwan da za su kawo cigaba.

Ganduje ya sha alwashin nuna goyon bayan sa ga sahihin zaɓe a jihar. Rahoton The Street Journal

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zabe, Sarkin Kano Ya Fito Fili Ya Gayawa Mutanen Jihar Abinda Yakamata Su Yi a Zaben Gwamna

Alhaji Aminu Dantata Ya Musanta Goyon Bayan Dan Takarar Ganduje

A wani labarin na daban kuma, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana goyon bayan Nasiru Gawuna a zaɓen gwamnan jihar Kano.

Dattijon ƙasa kuma hamshaƙin attajirin yace shi uba ne domin haka baya goyon bayan kowane ɗan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel