Gwamna Kwara Ya Samu Tagomashi Dan Takarar Gwamna Ya Janye Masa Takara

Gwamna Kwara Ya Samu Tagomashi Dan Takarar Gwamna Ya Janye Masa Takara

  • Yunkurin sake ɗarewar kujerar gwamnan jihar Kwara da gwamna Abdulrahman Abdulrazaq yake yi ya samu gagarumin tagomashi
  • Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) ya janye takara inda ya marawa gwamnan baya
  • Ɗan takarar na jam'iyyar YPP yace hakan da yayi ya zama wajibi domin ciyar da jihar gaba

Jihar Kwara- Ɗan takarar gwamnan jihar Kwara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Young Progressives Party (YPP), Waziri Yakubu Gobir, ya janyewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.

Waziri Yakubu Gobir a bayyana cewa ya janye ne saboda kishin jihar da yake yi. Rahoton The Punch.

Gwamnan Kwara
Gwamna Kwara Ya Samu Tagomashi Dan Takarar Gwamna Ya Janye Masa Takara Hoto: The Punch
Asali: UGC

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis bayan ya sanya labule da gwamnan jihar, Gobir ya bayyana cewa sun tattauna sosai da gwamna Abdulrazaq a cikin makonnin da suka gabata kan yadda za su ciyar da jihar gaba.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Balle Daga Hadakarta Da Jam'iyyar Peter Obi, Ta Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

A cewar sa, ta bayyana cewa hanyar da ta fi dacewa mu cimma muradun da muke so itace yin haɗaka da aiki tare. Rahoton Leadership

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A dalilin hakan, jami'iyyar Young Progressives Party (YPP) ta koma bayan gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Abdulrahman Abdulrazaq, a zaɓen gwamnan dake tafe."
"Ina tabbatar muku da cewa ban yanke wannan hukuncin cikin sauri ba. Na cimma sa ne bayan kwashe makonni muna tattaunawa da gwamna inda daga ƙarshe muka cimma matsayar zai yi aiki da wasu manufofi na haɗe da nasa manufofin domin ciyar da jihar gaba."
"A wannan yarjejeniyar, na yi amanna cewa idan gwamnan ya lashe zaɓe, zai kafa gwamnatin da zata yi aiki da waɗanda suka mara masa baya ciki har da mambobin jam'iyyar mu."

...Yace.

Janyewar Gobir daga takara na zuwa ƙasa da sa'o'i 24 bayan ɗan takarar majalisar wakilai a inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, Wahab Issa, da wasu ƙusoshin jam'iyyar sun sauya sun tsallaka zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Jam’iyyun Siyasa 4 Ke Shirin Maja Don Tsige Gwamnan APC a Wata Jihar Arewa

Yayan Uwar Gawuna, 'Dan Majalisar APC, ‘Yan ADP, Sun Shiga Jam’iyyar NNPP a Kano

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar NNPP ta samu tagomashi a Kano, jiga-jigan APC sun koma cikin ta.

Daga cikin waɗanda suka koma NNPP a Kano hada ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel