Dan takara
Ana ganin Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ne kurum 'yan takara a zaben 2023. Amma su Manjo Al-Mustapha su na daukar hankalin mutane.
A maimakon tsohon Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed A. Abubakar ya bi bayan AVM Sidique Abubakar mai ritaya, yana tare da Gwamna Bala Mohammed ne a zaben 2023.
A yau ne aka ji labari Ben Kure ya sanar magoya baya na da kuma abokan tafiyarsa a siyasa cewa ya sauka daga shugaban jam’iyyar NNPP na reshen jihar Kaduna.
A Taraba, Shugabannin Jam’iyyar Labour Party sun dakatar da Shugabar LP. Shugabar da aka dakatar daga ofis har na tsawon watanni 6 ta ce sharri ake yi mata
A jihar Neja, Asiwaju Bola Tinubu ya samu gudumuwar motoci da ofisoshin yakin neman zaben shugaban kasa daga wajen Sanata Sani Musa da Muhammad Idris Malagi.
Za a ji kwamitin yakin neman zaben APC ya yi karin haske kan abin da ya faru a wajen yawon kamfe a Neja domin Bola Tinubu ya bar wajen kamfe kafin a tashi taro.
A cikin daren yau, mai neman mulkin Najeriya a inuwar APGA, Farfesa Peter Umeadi ya kai ziyara zuwa gidan 'dan takaran jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso.
Dazu ne muka samu labari a shafin Facebook cewa wani daga cikin ‘yan tawagar motocin Atiku Abubakar ya tsere bayan gwabje motar Mai magana da yawun Bola Tinubu.
Ganin ana kamfe, Peoples Democratic Party, Social Democratic Party, Africa Democratic Congress da African Democratic Party sun yi tir da CBN kan dokar cire kudi
Dan takara
Samu kari