Rikicin Kamfe: Tinubu Ya Saduda, Zai Ba APC, Gwamnoni Kujeru 2000 a Kwamitinsa

Rikicin Kamfe: Tinubu Ya Saduda, Zai Ba APC, Gwamnoni Kujeru 2000 a Kwamitinsa

  • Da alama ‘Dan takarar shugaban kasa na APC zai busa bayan ya ciza a shirin yakin neman zaben 2023
  • Asiwaju Bola Tinubu zai amince a kara mutane a kwamitin da za su taya shi takarar shugaban kasa
  • Tinubu zai yi hakan ne domin ya tafi da Gwamnoni da Shugabannin APC da ke ganin ba a damawa da su

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasan Najeriya a karkashin APC, Asiwaju Bola Tinubu yana tunanin kara sunayen mutane a cikin kwamitin kamfe.

Rahoton da muka samu daga Punch a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba 2022, ya nuna ana maganar za a karo sunayen mutane 2000 a kwamitin.

‘Dan takaran za iyi wannan ne domin ya shawo kan shugabannin APC na kasa da kuma gwamnonin jihohin da ke kukan an yi watsi da mutanensu.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi Ya Ragargaji Gwamnatin APC a gaban Majalisar Dinkin Duniya

Wannan na zuwa ne bayan an fara rade-radin Abdullahi Adamu ya zargi ‘dan takaran da yin abubuwa ba tare da ya hada da majalisar NWC ba.

Ko da jam’iyyar APC ta musanya wannan, amma tun farkon makon nan aka tabbatar da gwamnoni ba su ji dadin ganin 'yan kwamitin da aka fitar ba.

Bayan kwamitin yakin neman takaran ya fito da sunayen mutane 422 da za su taya su kamfe, sai aka ji Hon. James Faleke yana cewa jerin bai cika ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu
Bola Tinubu a gaban kwamitin APC Hoto: @/officialasiwajubat
Asali: UGC

Za a kara yawan mutane

Wata majiya tace dole sai an kara adadin mutane da yawan kwamitocin da za suyi aikin yakin kamfe na zaben shugaban kasa da za ayi a farkon 2023.

A karkashin kwamitin yada labarai da sadarwa, Bayo Onanuga da mutane uku ko hudu kurum aka sa, majiyar tace su kadai ba za su iya wannan aiki ba.

Kara karanta wannan

Kwararan Majiyoyi Sun Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa APC Ta Dakatar Da Fara Kamfen Har Sai Baba Ta Gani

Nan gaba za a kara mutane fiye da 100 a karkashin kwamitocin da ake da su. Wannan zai sa adadin ‘yan kwamitin ya karu daga 422 da ake da su.

Jaridar ta rahoto wani babba a tafiyar Bola Tinubu yana cewa akwai karin mutanen da za a kawo domin su taya jam’iyyar APC lashe zaben shugaban kasar.

Zargin NWC ba gaskiya ba ne - Keyamo

Akwai ‘yan majalisar APC NWC da suke kukan ba a ba su damar duba jerin ‘yan kwamitin ba, sai dai kurum suka ji sakataren kamfe ya fitar da sunaye.

Festus Keyamo wanda ke magana da yawun bakin kwamitin zaben, ya musanya wannan zargi, amma ya tabbatar da za a fito da karin sunaye nan gaba.

Atiku ya soma kamfe

A makon nan ne kuma muka samu rahoto da yace kwamitin takarar Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa yace akwatin zabe kurum yake hange yanzu.

Daniel Bwala wanda shi ne kakakin Kwamitin yakin zaben yace babu wani abin da zai janye masu hankali. Wannan raddi ne ga masu neman tada rikici.

Asali: Legit.ng

Online view pixel