Yadda Atiku Zai Bi Wajen Maganin Akidar Biyafara Da Tayi Shekara da Shekaru

Yadda Atiku Zai Bi Wajen Maganin Akidar Biyafara Da Tayi Shekara da Shekaru

  • Atiku Abubakar mai neman takaran shugaban kasa a inuwar PDP zai yi maganin masu kukan Biyafara
  • Alhaji Atiku Abubakar yace za a canza fasalin kasa ta yadda jihohin kasar nan za su yi karfi a mulkinsa
  • Idan aka rage karfin gwamnatin tarayya, ‘dan takaran yana ganin za a daina kukan a raba Najeriya

Enugu - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takaran shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar yayi alkawarin kawo karshen fafatukar Biyafara.

Gidan talabijin na Arise TV ya rahoto Alhaji Atiku Abubakar yana cewa zai canza fasalin kasar nan ta yadda duk masu neman barkewa za su canza tunani.

Ana fama da mutanen da suke rajin kafa kasar Biyafara mai ‘yancin-kai a kudu maso gabashin Najeriya, ‘dan takaran yana fatan magance wannan matsala.

Da yake jawabi a wajen taron jam’iyyar PDP a jihar Enugu, Atiku Abubakar yace ba a duba takaitattun matsalolin da kowane bangare yake fama da shi a yau.

Kara karanta wannan

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

Kan jama'a ya rabu sosai

‘Dan takaran ya shaidawa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar hamayya ta PDP cewa an raba kan ‘yan kasar nan, ya yi alkawarin zai zama mai tafiya da kowa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan Atiku ya karbi mulki, yace zai yi bakin kokarinsa na ganin ya zama mai adalci da gaskiya. A cewarsa, ba a taba yin lokacin da kai ya rabu irin yanzu ba.

'Dan takaran PDP
'Dan takaran PDP, Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

A rahoton da Premium Times ta wallafa, ‘dan takaran shugaban kasar yace dole ne a dama da yankin kudu maso gabas idan ana son gyara tattalin Najeriya.

Sai an yi wa tsarin gwamnati gyara

Sauya fasalin kasa da yadda ake gudanar da gwamnati yana cikin burin Atiku Abubakar, wanda yace dokar kasa ta ba gwamnatin tarayya karfi da yawa.

Wazirin Adamawa yana ganin zai yi kyau a rage ikon gwamnatin sama, sai a karawa jihohi karfi. Atiku zai cin ma wannan manufa ne da hadin-kan majalisa.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

An rahoto Atiku mai shekara 75 yana cewa idan aka yi haka, jihohi za su maida hankali kan abin da ya shafe su, gwamnatin tarayya ta ji da aikin gabanta.

Da haka ne duk wani yanki mai kukan ba ayi da shi zai ji an ba shi dama. 'Dan siyasar yana ganin rashin wannan ne yake jawo wasu ke kukan raba kasa.

Mun tsallaka wajen Tinubu - 'Yan NNPP

Wasu jiga-jigan NNPP da aka hana takara sun ce jam'iyyarsu ba za ta lashe zabe ba. Kun ji labari cewa a maimakon su yi biyu-babu, suka ce sai suka bi APC.

Clement Bamigbola da mutanensa a jihar Osun yace sun bi bayan ‘dan takaran jam'iyya mai mulki, Bola Tinubu ganin cewa kwandon kayan dadi ya kife

Asali: Legit.ng

Online view pixel