Daga Bude Kamfe, Jam’iyyar LP Ta Bada Akawun Domin Tarawa ‘Dan Takararta Kudi

Daga Bude Kamfe, Jam’iyyar LP Ta Bada Akawun Domin Tarawa ‘Dan Takararta Kudi

  • Jam’iyyar Labour Party ta fitar da sanarwar bude kofar karbar gudumuwar kudi domin yakin neman zabe
  • An bada asusun yakin neman zaben shugaban kasa da nufin Peter Obi ya kai labari a takaran da yake yi
  • Jim kadan da bude kofar kamfe da asusun neman gudumuwar, wasu masoya sun fara aikawa da kudinsu

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta Labour Party ta nuna da gaske ta shiga zaben 2023, inda aka ji ta fara neman gudumuwa daga magoya baya.

Legit.ng ta kawo rahoto a safiyar Juma’a, 30 ga watan Satumba 2022, wanda ya bayyana cewa jam’iyyar ta fara karbar gudumuwar kamfe.

A wata sanarwa a shafin Twitter, LP ta bada lambar asusun banki ga magoya baya da masu fatan alheri da ke sha’awar taimakawa jam’iyyar.

Duk mai bukatar aika kudi domin takarar Obi a zaben 2023, zai yi amfani da wannan dama.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa

An fara kamfe a Najeriya

Rahoton yace jam’iyyar ta fitar da bayanin asusun bankin ne jim kadan bayan hukumar INEC ta yaye zanin da ta sa na yakin neman zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga ranar Alhamis dinnan aka bude kofar neman takarar shugaban kasa, wannan karo, ‘yan takara za su shafe kusan watanni biyar ana kamfe.

Peter Obi
Mabiya Peter Obi wajen kamfe a Jos Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Mun yi gaba - LP

Da karfe karfe 10:42 na dare LP ta aika sako a Twitter, wanda yake dauke da neman gudumuwa domin kuwa ba a shiga yakin zabe sai da kudi.

Kamar yadda hoton neman gudumuwar ya nuna, za a tara kudin kamfe a asusun Labour Party Fund Raising Account da ke bankin Zenith Bank.

“Asusun jam’iyyar Labour Party na kamfe”

"Labour Party Fund Raising Account

Zenith Bank

1225832294.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Tun a daren, har mutane sun fara aikawa da gudumuwarsu da nufin taimakawa Obi da jam’iyyarsa a neman yakin zaben shugabancin kasa.

Daga mai N1, 000, N10, 000 har zuwa N100, 000, jam’iyyar hamayyar za ta gudumuwar jama’a. APC tayi irin wannan ta hanyar saida kati a 2015.

"Bola Tinubu garau yake"

Dazu aka ji labari, wani babba a tafiyar APC kuma na kusa da ‘dan takaran APC, ya fadi yanayin da ya ga Bola Tinubu ana daf da zai bar Najeriya.

Duk da ya tare a kasar Ingila alhali an soma kamfen shugaban kasa, ana kyautata zaton ‘Dan takaran a 2023 garau yake, bai kwanta wani ciwo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel