Dattawan Arewa Sun Gindaya Sharadin Goyon Bayan ‘Dan takaran Shugaban Kasa

Dattawan Arewa Sun Gindaya Sharadin Goyon Bayan ‘Dan takaran Shugaban Kasa

  • Kungiyar Northern Elders Forum tace sai ta zauna da ‘yan takara kafin ta yanke shawara a kan 2023
  • Dr. Hakeem Baba-Ahmed yace za NEF za ta jijjiga 'yan takara irinsu Bola Tinubu da Atiku Abubakar
  • Dattawan Arewa sun yi alkawarin ba za su maimaita kuskuren da aka yi a 2015 a zabe mai zuwa ba

Abuja - A daren yau, aka ji kungiyar nan ta Northern Elders Forum ta Dattawan Arewacin Najeriya tana bayanin yadda za ta fito da wanda za ta goyi baya.

Kakakin kungiyar NEF a Najeriya, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya yi hira da gidan talabijin Channels, inda yace za su duba ‘yan takaran shugabancin kasar.

Hakeem Baba-Ahmed yake cewa dattawan yankin Arewa ba za su maimata kuskuren da suka yi a zaben 2015 ba, kowa ya bi bayan Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Barin Najeriya, Masoyan ‘Dan Takara Sun Fito da Shirin da Suke yi

Da yake bayani a shirin siyasa na Politics Today, dattijon yake cewa za su yi wa Atiku Abubakar, Bola Tinubu da irinsu Peter Obi gwaji, kafin su tsaida matsayarsu.

‘Dan takaran Shugaban Kasa
‘Dan takaran APC, Bola Tinubu a Masallaci Hoto: @gboyegaakosile
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar dattijon, za su yi wannan aiki ne domin gane wanda ya fi cancanta mutanen bangaren Arewacin Najeriya su marawa baya ya zama shugaban kasa.

An yi an gama - Inji Kakakin NEF

“Alkawarin da muka dauka cewa ba za muyi a wannan karo ba shi ne maimaita kuskuren 2015, mu ce babu wanda za mu zaba ‘Sai Baba.
Mu ka raka shi (Muhammadu Buhari) zuwa fadar Aso Villa, amma muka gagara zaunar da shi, mu tambaye shi abin da yake shirin yi.
Wannan karo mutum ba zai fada mana zai inganta tattallin arziki, ya inganta tsaro, ya yaki Boko Haram ba, dole ya yi bayani da kyau.

Kara karanta wannan

Bayan Tsame Hannu Daga Kamfen Atiku, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Yuwuwar Fice Wa Daga PDP

- Dr. Hakeem Baba-Ahmed

Wanene NEF ta ke hange?

Da aka tambayi, Baba-Ahmed a kan wanda zai dace da abin da NEF ta ke nema, Punch ta rahoto shi yana cewa ba su da wani ‘dan takara a cikin ransu.

“Ba za mu tsuke kanmu a kan yankin da ‘dan takara ya fito ba. Ni ke magana da yawun dattawan Arewa, ba mu taba cewa sai ‘Dan Arewa kurum za muyi la’akari da su ba.
Ban san game da sauran yankunan kasar nan ba, amma ‘yan Arewa ba za su zabi mutum ba, har sai mun gamsu ya shirya wajen yadda zai magance matsalar Najeriya.”

- Dr. Hakeem Baba-Ahmed

Jirgin Atiku Abubakar ya iso

Dazu nan muka ji labari Bola Tinubu da Abokin takararsa, Kashim Shettima sun lula Landan. ‘Yan takaran sun yi tafiya ne ana daf da soma kamfe a Najeriya.

Bayo Onanuga ya fadi lokacin da ‘dan takaran na jam’iyyar All Progressives Congress zai dawo gida, za a fara yakin kamfe Tinubu yana ketare inda za su huta.

Kara karanta wannan

Shugaban CAC Ya Fadawa Kiristoci Wanda Ya Kamata Su Ba Kuri’arsu a Zaben Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel