Ana Samun Rabuwar Kai a Kamfe Saboda Tinubu Ya Jawo Gwamna, Ya Ba Shi Mukami

Ana Samun Rabuwar Kai a Kamfe Saboda Tinubu Ya Jawo Gwamna, Ya Ba Shi Mukami

  • Wasu kungiyoyi na magoya baya jam’iyyar APC da masoyan Bola Tinubu sun rabu a kan Yahaya Bello
  • Bola Tinubu mai takarar shugaban kasa ya zabi Gwamna Yahaya Bello ya jagoranci matasa wajen kamfe
  • Yayin da wasu ke ganin an yi daidai da aka dauko Gwamnan na Kogi, wasu sun soki zabin da APC ta yi

Abuja - Wasu kungiyoyin jam’iyyar APC suna ta samun sabani da junasu tun kafin tafiyar yakin neman zaben shugabancin Najeriya na 2023 tayi nisa.

Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya tabbatar da kungiyar Asiwaju Students Campaign Organisation ta ji haushin ba Yahaya Bello mukami a APC.

Wannan kungiya ta dalibai masu goyon bayan Bola Tinubu da Kashim Shettima a 2023 ba ta ji dadin nada gwamnan ya jagoranci matasa a kamfe ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

Folarin Tejumola wanda yana daya cikin jagororin wannan tafiya, ya shaidawa manema labari ba kishin jam’iyya ta sa aka ba Bello wannan aiki ba.

Ana bukatar sabon jini ne a 2023 - Kungiya

Mista Tejumola ya yi tir da yadda ake yawan zagayawa da shugabanni a Najeriya, a maimakon a dauko matasa masu sabon jini domin a rika damawa da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ya kamata APC ta fahimci wannan zaben ya sha bambam da sauran zabuka da aka rika yi, muna neman wanda zai iya tafiya da matasan Najeriya ne.
Ba mu bukatar irin Gwamna Bello, wanda yana cikin tsarin, bai damu da matsalar matasa ba.

- Folarin Tejumola

Asiwaju Bola Tinubu
Bola Tinubu da Gwamna Yahaya Bello Hoto: nannews.ng
Asali: UGC

An yi daidai inji APC Young Stakeholders

Ana haka kuma sai ga ‘yan kungiyar APC Young Stakeholders suna cewa dauko Gwamnan Kogi da aka yi, ya nuna Tinubu zai tafi da matasa a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Yadda Wani Gwamna da Ayu suka Kitsawa Wike Kullaliya inji Jang

Mun samu rahoto da yace Kakakin wannan kungiya, Aliyu Audu yace Yahaya Bello ya fi kowa cancanta ya jagoranci matasa wajen yi wa Tinubu yakin zabe.

Saboda shi Gwamna ne? - PSC

Kafin nan, labari ya zo daga This Day cewa kungiyoyin matasa kimanin 300 a karkashin inuwar Presidential Support Council (PSC) ba su tare da Gwamnan.

Shugaban wannan kungiya a Najeriya, Dr Kassim Muhammad ya kira taron manema labarai a garin Lafia, yace an dauko Bello ne saboda yana rike da mulki.

Kassim Muhammad yana ganin Tinubu ya yi kuskure wajen dauko wanda aiki ya yi masa yawa.

Babu zaman lafiya a PDP

Kun ji labari cewa Cif George ya dage sai Iyorchia Ayu ya cika alkawarin da ya yi a gaban Duniya tun kafin zaben ‘dan takaran shugabancin kasa na PDP.

Sannan tsohon ‘dan siyasar yace Atiku Abubakar bai tuntube su ba, sai kawai ya fitar da wadanda za su yi masa aikin yakin neman takarar shugaban kasa

Kara karanta wannan

Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel