Kwamitin kamfe Ya Yi Martani ga Gwamnonin APC da Suka yi Fushi da Bola Tinubu

Kwamitin kamfe Ya Yi Martani ga Gwamnonin APC da Suka yi Fushi da Bola Tinubu

  • Sabuwar sanarwa ta fito daga kwamitin APC na yakin neman zaben Bola Tinubu da Kashim Shettima
  • Hon. James Faleke ya bayyana cewa ba suyi da sunayen da gwamnonin jihohi suka kawo masu ba
  • Sakataren kwamitin takaran yace nan gaba za a sake fito da sunayen ‘ya ‘yan kwamitin yakin zaben

Abuja - Sakatare a kwamitin APC na yakin neman zaben shugaban kasa, James Faleke, yayi magana game da jerin ‘yan kwamitin takaran da aka fitar.

Hon. James Faleke yace sunayen mutane 422 da aka saki a karshen makon da ya wuce, bai nufin an kammala fitar da sunayen ‘yan kwamitin neman zaben.

The Cable tace jawabin Faleke ya zo ne bayan ji rahotanni su na yawo wasu gwamnonin APC suna kuka a kan yadda aka yi watsi da sunayen da suka mika.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Za Ta Fara Yakin Neman Zabe da Addu’o’in Musamman na Neman Sa’a

Da yake magana a madadin kwamitin neman zaben shugaban kasar, Hon. Faleke yace ba cikakken jerin ‘yan kwamiti aka fitar ba, akwai ragowa na nan tafe.

Rahoton Tribune yace nan gaba za a kara bada sanarwar sauran wadanda za su taimakawa takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben da za ayi a 2023.

Asiwaju Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu yana neman tikiti Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda gaskiyar lamarin yake - PCC

“Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC yana mai fayyace cewa sunayen kwamitin da aka fitar a karshen mako bai cika ba.
“Majalisar takarar tana tabbatar da Masu girma Gwamnoninmu ‘yan kwamitin takarar ba suyi watsi da sunayen da suka gabatar mana ba.
Wasu daga cikin wadanda gwamnoni suka bada sunayensu, sun samu shugabanci a kwamitoci, sunayen wasu zai fito a wasu bangarorin.”

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnoni ba su ji dadin ganin yadda aka yi fatali da sunayen da suka bada a kwamitin kamfe ba, aka dauko wasu daga jihohin.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno APC, Gwamnonin Jam’iyya na Shirin Yi wa Bola Tinubu Zagon kasa

Majiyar mu ta shaida mana za a kafa irinsu bangare na harkar hadakar addinai wanda zai kunshi malaman Islama da Kirista da za su bada gudumuwa.

Akwai kura a APC

Dazu da safe, an karanta labari cewa Kungiyar gwamnonin jihohin APC (PGF), suna zargin an yi watsi da mafi yawan mutanen da suka ce a sa a aikin kamfe

A Kwara, an cika kwamitin na mutum 422 da wadanda suka fito daga karamar hukuma guda, mutum daya ya samu shiga a wadanda gwamna ya bada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel