Takarar Tinubu ta Gamu da Cikas, Manyan Yarbawa na Neman Raba Kuri’un APC

Takarar Tinubu ta Gamu da Cikas, Manyan Yarbawa na Neman Raba Kuri’un APC

  • Pa Ayo Adebanjo ya na neman kashewa Bola Tinubu kasuwa a 2023, yana goyon bayan Jam’iyyar LP
  • Shugaban na Afenifere da irinsu Olu Falae su na goyon bayan Ibo ya zama Shugaban Najeriya
  • ‘Yan Afenifere Renewal Group sun sha banbam, sun ce Tinubu ya fi cancanta Yarbawa su ba kuri’u

Nigeria - Ra’ayoyin manyan kasar Yarbawa ya rabu a kan wanda mutanen Kudu maso yamma za su marawa baya ya zama shugaban kasa.

Vanguard ta rahoto cewa Pa Ayo Adebanjo na kungiyar nan ta Afenifere, yana ganin Peter Obi na LP ne ya cancanta ya karbi shugabancin Najeriya.

Haka zalika Cif Olu Falae wanda ya yi takarar shugaban kasa a 1999 yana goyon bayan Obi, ya kuma ce Afenifere ba ta dauki matsaya ba tukun.

Kara karanta wannan

'Dan takaran 2023 Ya yi Sabon Zama da Obasanjo, An yi Kus-kus 'a kan batun kasa'

Da alama kungiyar dattawan Yarbawa ta Yoruba Council of Elders da Afenifere Renewal Group wanda aka sani da ARG za su bi Bola Tinubu.

Shugaban Afenifere yana goyon bayan LP

Shugaban Afenifere, Ayo Adebanjo ya shaidawa manema labarai a garin Legas cewa ba za su goyi bayan Bola Tinubu saboda kurum yana Bayarabe ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattijon yace tun tuni ra’ayinsa shi ne a ba ‘Yan kudu maso gabas dama su rike Najeriya, don haka kungiyarsu take marawa Peter Obi baya a 2023.

Asiwaju Bola Tinubu
'Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Afenifere ba ta da 'dan takara tukuna

Jaridar ta rahoto Olu Falae yana cewa bai san matsayar Afenifere ba, amma shakka-babu, zai goyi bayan mulkin Najeriya ya koma kudu maso gabas.

Falae yake cewa Afenifere ba ta tsaida ‘dan takararta ba tukuna, amma yace duk matsayar da aka dauka, shi yana goyon bayan ‘dan takaran na LP.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Barin Najeriya, Masoyan ‘Dan Takara Sun Fito da Shirin da Suke yi

Amma Sakataren kungiyar YCE, Dr. Kunle Olajide, yace babu ruwansu da Afenifere, yace za suyi zama kafin su fadawa jama’ansu wanda za su zaba.

APC za ta kare ra'ayin Yarbawa - ARG

Ita kungiyar Afenifere Renewal Group wanda ta balle daga Afenifere tace ‘dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu ne zabinta a zabe mai zuwa.

Shugaban ARG na kasa, Wale Oshun yace Tinubu ne wanda zai kare martabar Yarbawa, yace suna gudun maimata kuskuren da suka yi a 2010.

Shi kuwa shugaban Ilana Omo Oodua, Farfesa Banji Akintoye bai damu da zabe ba, abin da yake gabansa shi ne kasar Yarbawa su balle daga Najeriya.

Obasanjo yana goyon bayan Obi?

Dazu kun ji labari Peter Obi da Olusegun Obasanjo sun sa labule a karo na uku a cikin watanni uku. Da alama suna shiryawa zaben shugaban kasa ne.

Bayan ya ziyarci tsofaffin shugaban Najeriya a garin Minna, an ga ‘Dan takaran a gidan Obasanjo da ke jihar Ogun kamar yadda aka yi a watan Yuli.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel