Jerin Abubuwa 11 da Za Su Yi Tasiri Wajen Wanda Zai Zama Shugaban kasa a 2023

Jerin Abubuwa 11 da Za Su Yi Tasiri Wajen Wanda Zai Zama Shugaban kasa a 2023

Abuja – Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa cibiyar CDD tayi nazarin zabe mai zuwa, inda ta fahimci shi ne zaben da zai fi kowane wahala

Legit.ng Hausa tayi kari a kan rahoton, ta karo abubuwan da ake tunani za suyi tasiri a zaben da za a shirya nan da watanni biyar a fadin kasar nan.

Wasu abubuwa ake ganin za suyi tasiri?

1. Rashin Buhari a ‘yan takara

Tun 2003, ba a taba yin wani zabe a Najeriya da Muhammadu Buhari bai shiga ba, sai wannan karo. Za a zura idanu domin ganin wa zai gaje mabiyasa.

Yadda miliyoyin mabiyansa suka yi zabe za iyi tasiri a wanda zai zama sabon shugaban Najeriya.

2. Babu tsohon soja da yake takara

Kara karanta wannan

Wani Sabon Hasashe Ya Tabbatar da Tinubu, Atiku Ba Za Su Lashe Zaben 2023 ba

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Inda wannan zaben ya sha ban-bam shi ne babu wani tsohon soja da a manyan ‘yan takaran. Akasin abin da aka gani a 1999, 2003, 2007, 2011, 2015 da 2019.

Ana cewa tsofaffin sojoji suna da ta-cewa a wajen kawo wanda zai mulki mutanen kasar nan tun daga zaben tsaida gwani a manyan jam'iyyun siyasa.

3. Shugaba mai-ci

Tun bayan 2007 babu wani zabe da aka yi wanda shugaban kasa mai-ci ba ya takara sai wannan karo. Hakan ya sa ba a iya saurin gane wanda zai yi nasara.

‘Yan takaran za su shiga zaben ne suna neman mulki a karon farko, ko da wasu sun saba takara.

4. Sababbin tsare-tsare

A zaben 2023, hukumar INEC za tayi amfani ne da sabuwar dokar zabe wanda aka sa hannu a 2022. A wannan karo ne dokar za tayi aiki a babban zabe.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

Wannan doka za tayi tasiri sosai wajen zabe da kuma shari’a da za ayi a kotu bayan an yi zaben.

5. Ma’aikatan zabe

CDD tace wani abin damuwa shi ne aikin da ke gaban jami’an INEC na gudanar da zabe a rumfuna 176, 846, a maimakon 56, 872 da aka yi amfani da su a 2019.

Wannan ya sa hukumar ta soma horas da mutane miliyan 1.4 domin shiryawa aikin zaben da zai ci karo da rashin tituna da karancin wutar lantarki a Najeriya.

APC ta tsiada Tinubu
APC ta tsiada Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

6. Rashin tsaro

Shakka babu akwai matsalar tsaro a jihohi da-dama, wannan zai yi tasiri a zaben 2023. Ana tunani akwai yankunan da ba za a iya zabe ba saboda matsalar.

A Arewa maso gabas akwai hadarin Boko Haram, a Arewa maso yamma akwai inda ‘yan bindiga sun yi karfi, sannan IPOB tana da karfi a Kudu maso gabas.

7. Adadin ‘yan takara

An saba shiga zabe da ‘yan takara barkatai a Najeriya, amma a 2023 abin ya canza. Jam’iyyu 18 za a gwabza da su a zaben, manya su ne APC, PDP, LP da NNPP.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Gindaya Sharadin Goyon Bayan ‘Dan takaran Shugaban Kasa

Duka manyan ‘yan takaran sun taba zama a karkashin jam’iyyar APC ko PDP. Masu nazarin siyasa sun fi kawo Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi a lissafi.

8. Addini

Wannan karo jam’iyyar APC ta tsaida Musulmi da Musulmi wanda ake ganin zai jawo mata goyon bayan ‘Yan Arewa da fushin wasu yankunan kudancin Najeriya.

A manyan ‘yan takara, Peter Obi na LP ne kadai Kirista. Jam’iyyar NNPP ta tsaida Fasto da nufin samun goyon baya. Malaman addini za su samu ta-cewa a 2023.

9. Kananun jam’iyyu

Tun 1999, an saba ganin zaben shugaban kasa ya kasance tsakanin jam’iyyu biyu. Amma wannan karo LP da NNPP suna shirin kawowa APC da PDP ciwon kai.

Peter Obi da Rabiu Kwankwaso za su batawa Atiku Abubakar da Bola Tinubu lissafi a 2023.

10. Kudi

Duk da farfadowar kananan jam’iyyu, Legit.ng Hausa ta fahimci siyasar kudi za ta iya aiki a zaben 2023. An koma sayen kuri’u tun da murde zabe yana rage sauki.

Kara karanta wannan

Shi fa uba nane: Tsohon gwamna daga Arewa ya yi tattaki, ya gana da Obasanjo har gida

Manyan ‘yan takara da jam’iyyu masu mulki suna da kudin batarwa wajen jan ra’ayin mutane.

11. Mulki ya komawa Ibo

Akwai masu ganin ya kamata mulki ya je yankin Kudu maso gabas domin babu Ibo da ya shiga Aso Villa tun da aka dawo tsarin mulkin farar hula a Mayun 1999.

Ibo ba ta da ‘dan takarar shugaban kasa ko na mataimaki a duka manyan jam’iyyun nan na APC, PDP da NNPP illa a LP wanda ta tsaida tsohon gwamnan Anambra.

Baraka a APC?

An ji labari kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya yi karin haske a kan abin da ya fusata wasu daga cikin Gwamnonin Jam’iyya

A wani jawabi da aka fitar, James Faleke ya ba gwamnonin da ke fushi amsa, yace za a fadada kwamitin takarar da sunayen mutanen da suka bada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel