Jigon PDP Ya Kara Ja Da Baya da Atiku, Yace Babu Tabbas a Kan ‘Dan Takaransu

Jigon PDP Ya Kara Ja Da Baya da Atiku, Yace Babu Tabbas a Kan ‘Dan Takaransu

  • Bode George yana ganin ba dole ba ne Atiku Abubakar ya dunkule ‘yan Najeriya idan ya samu mulki
  • Tsohon ‘dan siyasar yace ba a tuntube su ba, sai dai suka ji an fitar da sunayen ‘yan kwamitin kamfe
  • Cif George ya dage sai Iyorchia Ayu ya cika alkawarinsa na murabus, idan PDP ta kai takara Arewa a 2023

Lagos - Bode George ya bayyana cewa idan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ba za su iya hada-kansu a yanzu ba, babu tabbas Atiku Abubakar zai hada-kan al’umma.

Cif Bode George ya yi wannan bayani a lokacin da ya bayyana a shirin siyasa na gidan talabijin Politics Today a ranar Laraba, domin tattauna rikicinsu.

“Dan takaranmu yana cewa shi mai hada-kai ne. Idan ba za mu iya hada-kan jam’iyyarmu ba, a wannan matakin, menene tabbacin ya shirya hada-kan al’umma idan ya isa can. Idan ba haka ba, zai yi maganar tsarin mulki ne

Kara karanta wannan

Jonathan: Abin Da Ya Sa Na Kira Buhari a Waya Kafin a Gama Kirga Kuri’un 2015

Allah ya bada sa’a!

Bode George ya shaida cewa ba a tuntube shi kafin a zakulo ‘ya ‘yan PDP da za su yi wa Atiku Abubakar aikin yakin neman zabe a 2023 daga jihar Legas ba.

Daily Trust ta rahoto George yana cewa alamu na nuna shi kadai yake so ya yi wa kansa kamfe, idan kuwa haka abin yake, iyakarsu da shi fatan alheri a zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Iyorchia Ayu ya saba alkawarinsa

Kamar yadda bidiyon wannan hira ya nuna, George yace Sanata Iyorchia Ayu ya yi alkawarin zai sauka daga kujerarsa da zarar ‘Dan Arewa ne ya samu takara.

Shugaban PDP
Shugaban PDP a Najeriya, Sanata Iyorchia Ayu Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Tun da Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban kasa, ‘dan siyasar yace babu abin da zai hana Ayu ajiye mukaminsa na shugaban jam’iyya na kasa.

Bari in fadakar da mutane a kan batun nan; ba mu maganar a cire shi (Ayu) ko a tursasa masa (ya yi murabus).

Kara karanta wannan

Wike Ya Rasa Ƙashin-Baya a Rikicin PDP, Na Hannun Damansa Yace Atiku Zai Yi Wa Aiki

Shi da kan shi ya yi alkawari idan ‘dan takara ya fito daga Arewa (shi ya fada a gaban Duniya), zai yi murabus.

George: Babu adalci idan aka yi haka

A ra’ayin George, ganin cewa Muhammadu Buhari yayi shekara bakwai a mulki, kuma ta fito ne daga Arewa, bai dace wanda zai gaje ya zama ‘Dan Arewa ba.

Amma tun da hakan ta faru, sai shugaban jam’iyyar PDP ya fito daga yankin kudancin Najeriya, abin da shi da mutanensa ke rikici kenan a kai har yau.

Wike su dawo APC, su huta - FFK

Dazu aka samu rahoto Femi Fani-Kayode yace ya san za a zo irin wannan rana a PDP, yayi wa tsohuwar jam’iyyarsa kaca-kaca a kan batunsu Nyesom Wike.

Tsohon Ministan tarayyan wanda jama’a suka fi sani da FFK yace yanzu duk wanda ba ‘Dan Arewa ba, hoto ne shi a PDP, yake cewa babu adalci a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

Asali: Legit.ng

Online view pixel