Babban bankin Najeriya CBN
CBN ya ce ya shirya sayar da dala 10,000 ga kowanne d'an canji a kan N1101/$ sannan ya umurci da su siyar da su a kan karin da bai wuce kashi 1.5 ba.
Babbar kotun jihar Legas mai zama a Ikeja ta umarci EFCC ta tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele daga ranar Litinin, 8 ga Afrilu.
Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da Emefiele tare da Henry Isioma Omoile a gaban kotun mai shari’a Rahman Oshodi kan sabbin tuhume-tuhume 26.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya sallami wasu daga cikin ma'aikatansa har guda 50 a ci gaba da garambawul din ake yi a bankin. Akwai wasu da za a kora nan gaba.
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa EFCC ta sake shigar da sababbin tuhume-tuhume na cin hanci kan tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Bincike ya nuna cewa ikirarin da wasu suka yi a shafukan sada zumunta cewa Dala ta karye zuwa N650 a watan Afrilu ba gaskiya bane, har yanzu farashin ya haura N1000.
Dala ta kuma karyewa a kasuwar canji, $1 ta koma N1, 280 a kasuwar canji. Ribar N20 ne ‘yan canjin suke samu idan sun saida kowace dala a kasuwar bayan fage.
Yan canji sun musanta rahoton cewa Dala ta karye har an fara sayar da ita a kan N1000 kan kowace Dala ɗaya a kasuwa, sun ce a yanzu dai ta dawo N1,300.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya dauko bincike kan basussukan $7bn da tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele, ya bari. EFCC na cikin masu bincike.
Babban bankin Najeriya CBN
Samu kari