Gaskiya Ta Fito: Dalilin da Ya Sa Yan Majalisa 8 Suka Je wurin Tinubu bayan Sun Fice daga APC

Gaskiya Ta Fito: Dalilin da Ya Sa Yan Majalisa 8 Suka Je wurin Tinubu bayan Sun Fice daga APC

  • ’Yan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas da aka dakatar sun bayyana dalilin ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu
  • Sun ce sun tattauna da shugaban ƙasar kan dakatarwar da suka bayyana a matsayin matakin da ya saba wa doka
  • Ministan tsaro na ƙasa, Bello Matawalle, ne ya jagorance su zuwa wajen shugaban ƙasar domin shawo kan rikicin siyasar APC a Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - ’Yan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas da aka dakatar sun bayyana dalilin ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu.

Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da ’yan majalisar a watan Fabrairun 2024 bisa zargin karya dokokin majalisa da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Yan Majalisar Zamfara.
Yan Majalisar dokokin Zamfara 8 tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yadda yan Majalisar suka bar APC

Premium Times kuma ta ruwaito cewa ’yan majalisar da aka dakatar sun sanar kwanan nan cewa sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki, inda suka fara laluben jam'iyyar da za su koma.

Kara karanta wannan

Yan Majalisa 8 da suka bar APC sun canza shawara bayan haɗuwa da Shugaba Tinubu

Sai dai ’yan majalisar sun dage cewa dakatar da su da aka yi ya saɓa wa doka, lamarin da ya kara jan hankali a siyasar jihar Zamfara.

Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan lamarin, Karamin Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, ya jagoranci ’yan majalisar zuwa wajen shugaban ƙasa domin shawo kan rikicin siyasa da ke ƙara raba kan APC a Zamfara.

Ɗaya daga cikin ’yan majalisar da aka dakatar, Hon. Aliyu Kagara, wanda ya kasance shugaban marasa rinjaye a majalisar kafin dakatar da shi, ya tabbatar da cewa sun je wurin Tinubu.

Dalilin zuwan yan Majalisa 8 wurin Tinubu

Da yake tabbatar da lamarin ga NAN ta wayar tarho a ranar Litinin, ya ce:

“Eh, mun ziyarci Shugaba Bola Tinubu ne bisa gayyatarsa.”

Kagara, wanda ke wakiltar mazaɓar Talata Mafara ta Kudu, ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa shiga tsakani a lamarin, yana mai bayyana matakin a matsayin na uba.

Kara karanta wannan

Yadda tawagar ofishin Ribadu suka ceto mata, miji da jaririyarsu da aka sace

“Mun tattauna abubuwa da dama da shugaban ƙasa dangane da dakatar da mu daga Majalisar Dokokin Zamfara ba bisa ƙa’ida ba. Mun yi masa bayani dalla-dalla kan komai, kuma ya yi alƙawarin sake kiran wani taro domin tattauna batun.
“Dole ne mu kasance masu biyayya ga shugaban ƙasa. Ka sani, duk wani ɗan Najeriya nagari, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da yake ciki ba, dole ne ya girmama shugaban ƙasa.
“Har yanzu ba mu yanke wata shawara ba, kuma ba mu ɗauki wani mataki ba a yanzu. Muna jiran wata sabuwar gayyata daga shugaban ƙasa kamar yadda ya yi alƙawari,” in ji Kagara.
Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Yan Majalisar sun canza shawara

Kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa ’yan majalisar dokokin jihar Zamfara takwas da suka yi murabus daga jam’iyyar APC makonnin da suka gabata sun canza shawara.

An ruwaito cewa sun soke matakin da suka dauka na fita daga APC yayin da ake ɗaukar matakan magance korafe-korafensu bayan ganawar da suka yi da shugaban ƙasa Bola Tonibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262