Tinubu Zai Karbo Sabon Bashin Dala Biliyan 2.25 Daga Bankin Duniya

Tinubu Zai Karbo Sabon Bashin Dala Biliyan 2.25 Daga Bankin Duniya

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirin karbo sabon bashi na dala biliyan 2.25 a bankin duniya (WB)
  • Ministan kudin kasar ne, Wale Edun, ya tabbatar da nasarar samun karbar bashin kudin a birnin Washington DC yayin hira da 'yan jarida
  • Ya kuma bayyana matakan da gwamnati za ta dauka domin ganin ta biya bashin cikin sauki a cikin shekarun da aka shardanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da nasarar samun damar karbar bashin kudi har dala biliyan 2.25 daga bankin duniya (WB)

Shugaba Tinubu
Ministan kudi, Wale Edun ya ce Najeriya ta fitar da tsare-taren da biyan bashin ba zai zo da matsala ba. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ministan kudi, Wale Edun, ne ya sanar da hakan wa manema labarai a birnin Washington DC na kasar Amurka

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

A shekaru nawa za a biya bashin?

A cewar jaridar Vanguard, ministan ya yi bayanin ne bayan taron da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya shirya a Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya kuma kara da cewa Najeriya na daf da kammala shirye-shiryen karbar bashi mai saukin ruwa daga bankin bunkasa tattalin arzikin Afrika (ADB)

Jaridar the Guardian ta ruwaito cewa Mista Edun ya ce Najeriya za ta biya bashin ne tsawon shekaru 40 kuma an yi wa kasar sauki sosai a kan karin kudin ruwa.

Hanyoyin da za a biya bashin

Yayin da ya ke magana a kan yadda Najeriya za ta biya bashin, ya ce gwamnatin Tinubu ta na kokarin kara bunkasa kudin shiga wanda zai taimaka wurin biyan bashin cikin sauki.

A cewarsa, yanzu haka gwamantin Tinubu na kokarin kara yawan man fetur da kasar ke hakowa daga ganga miliyan 1.6 zuwa ganguna miliyan 2.

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

Ya kuma kara yin kira ga 'yan Najeriya mazauna ketare da su yi amfani da damar da suke da ita wajen habaka tattalin arzikin Najeriya.

Tinubu zai ci bashin dala biliyan 8.69

A wani rahoton kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar Majalisa don sake karbo bashin dala biliyan 8.69

Shugaban ya bukaci amincewar Majalisar ce don cika kudirin Gwamnati Tarayya na karbar bashin daga shekarar 2022 zuwa 2024

Asali: Legit.ng

Online view pixel