Kwamandan NSCDC Ya Fito da Bayanin Yadda Mutane 37 Suka Mutu a Hannun Hukumar
- Suberu Aniviye ya nemi afuwar iyalan mutum 37 da ake zargin masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun NSCDC
- Aniviye ya ce an kama mutanen ne bayan korafe-korafen mazauna yankin M.I. Wushishi kan ayyukan haƙar ma’adanai
- Kwamitin bincike ya ziyarci ɗakin ajiyar gawarwaki na Babban Asibitin Minna, inda aka bayyana cewa har yanzu ba a karɓi gawarwaki uku ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Suberu Aniviye, kwamandan rundunar Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja da aka dakatar, ya fito ya nemi afuwa.
Kwamandan na NSCDC ya nemi afuwar iyalan mutum 37 da ake zargin masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun hukumar.

Source: Twitter
A cewar gidan talabijin na NTA, Aniviye ya nemi afuwar ne yayin da yake bayar da shaida a gaban kwamitin bincike kan mutuwar mutanen a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Kara karanta wannan
2027: Shugaban INEC ya sanar da ma'aikatan hukumar abin da ba za su yarda da shi ba
Aniviye ya bayyana mutuwar a matsayin kuskure
Yayin zaman kwamitin na biyu, wanda Alƙali Mohammed Mohammed ke jagoranta, Aniviye ya roƙi iyalan mamatan da su yafe masa.
Ya bayyana abin da ya faru a matsayin babban kuskure mai tsada wanda za a iya kauce masa.
Aniviye ya ce an fara aikin ne bayan mazauna yankin M.I. Wushishi Housing Estate sun shigar da ƙorafe-ƙorafe kan ayyukan haƙar ma’adinai a yankunansu.
Ya bayyana cewa ya ziyarci wurin a ranar 15 ga Satumba, kafin ya tura jami’an sa-kai masu kula da harkokin ma’adinai, waɗanda suka kama waɗanda ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne a yammacin washegari.
Ya ce ya gano gawarwakin a ofishin hukumar
Kwamandan da aka dakatar ya ce ya samu labarin mutuwar waɗanda ake tsare da su ne ta hanyar kiran waya a ranar 17 ga Satumban 2026.
Ya ce bayan samun labarin, ya koma ofishin rundunar, inda ya tarar da gawarwakin suna kwance a ƙasan ɗakin da ake tsare da mutane.
Aniviye ya ce ya sanar da Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, wanda ya ba da umarnin a kai gawarwakin ɗakin ajiyar gawarwaki.
Ya ƙara da cewa ya tuntubi kwamishinan ’yan sandan jihar da daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).
A cewarsa, an shirya gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu a ranar 17 ga Satumba, amma mutuwarsu ta faru kafin hakan.
Wasu ma’aikatan NSCDC sun bayar da shaida
A yayin zaman kwamitin, Stephen Tsado, jami’in shari’a na NSCDC a jihar, da Maryam Etang, ma’aikaciyar jinya da ke aiki a sashen kula da lafiya na rundunar, su ma sun bayar da shaidarsu.
Bayan kammala zaman, Alƙali Mohammed ya jagoranci sauran mambobin kwamitin zuwa ɗakin ajiyar gawarwaki na Babban Asibitin Minna, inda aka ajiye gawarwakin mamatan.
Mohammed ya ce har zuwa ranar Alhamis, akwai gawarwaki uku da iyalansu ba su zo sun karɓa ba.
Abin da ya faru kafin mutuwar mutanen
A watan Satumba, mutum 37 da ake zargin masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ne sun mutu a hannun NSCDC bayan an kama su a ƙauyukan M.I. Wushishi da Lukoto da ke Jihar Neja.
A baya, Aniviye ya bayyana cewa an kama mutanen ne yayin wasu ayyukan da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Aniviye tare da bayar da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar mutanen.
Haka kuma, ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa mai mambobi 10 domin gano yanayin da ya jawo mutuwar waɗanda ake tsare da su.

Source: Original
NSCDC ta dakatar da jami'anta
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar NSCDC ta dakatar da wasu jami’anta uku kan mutuwar mutum 37 a Neja.
Ta kuma bayar da umarnin saukar da tutoci na tsawon kwana uku domin nuna alhini kan mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne.
Asali: Legit.ng

