Hukumar KADIRS ta Garkame Rassan Babban Banki 6 a Jihar Kaduna

Hukumar KADIRS ta Garkame Rassan Babban Banki 6 a Jihar Kaduna

  • Hukumar tattara kudin haraji a jihar Kaduna (KADIRS) ta garkame rassan wani babban banki guda shida da ke jihar saboda kin biyan haraji na miliyoyin naira
  • Hukumar KADIRS na zargin bankin da kin biyan haraji daga shekarar 2019-2021 wanda ya tasamma N14m, kuma bankin ya yi biris da tunatarwarsu
  • Aysha Muhammad, sakatariyar hukumar ta bayyana cewa kotu ta ba su damar rufe rassan bankin tare da neman diyyar wahalar da su ka sha wajen zirga-zirga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru shida. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna-Hukumar tattara kudin haraji ta jihar Kaduna (KADIRS) ta rufe wasu rassan wani babban banki guda shida saboda zargin kin biyan haraji ga gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

70% na fursunoni a Kano na jiran shari'a, suna samun ilimi a daure

Ana zargin hukumar bankin da kin biyan harajin da yawansa ya tasamma miliyan N14.3 miliyan.

Hukumar KADIRS ta rufe rassan bankin UBA saboda kin biyan haraji
Hukumar na bin bankin bashin da ya haura N14 miliyan Hoto: Kaduna State Internal Revenue Service
Asali: Twitter

A wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, an rufe bankunan ne bayan tunatar da su na tsawon lokaci amma su ka ki daukar mataki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun yi rakiyar rufe bankin

Sakatariyar KADIRS, kuma mai bawa hahukumar shawara kan harkokin shari’a, Barista Aysha Muhammad ce ta jagoranci rufe bankunan da rakiyar jami’an tsaro.

Aysha Muhammad ta kara da cewa kotu ce ta ba hukumar izinin garkame rassan bankin guda shida, inda kuma ta sahale masu karbar wasu makudan kudi da ake bin bankin.

A cewarta, ana bin bankin harajin da ya kai naira N14,367,322.20 miliyan daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Kotun ta kuma umarci bankin ya biya hukumar tattara harajin naira 250, 000 saboda jelen da su ka yi da su.

Kara karanta wannan

Kamfanin KEDCO ya yanke wutar asibitin Kano, masu haihuwa suna kwance

Har yanzu hukumomin bankin ba su ce uffan kan rufe rassansa guda shida a jihar Kadunan ba.

A cewar sakatariyar, daukar mataki kan bankin na daga kokarinsu na tabbatar da tattara harajin naira N120 biliyan, kamar yadda PM News ta wallafa.

Gwamnati ta ba bankuna umarni kan ATM

Mun ruwaito mu ku cewa Gwamnatin tarayya ta umarci bankuna su raba katin cirar kudi, watau ATM kyauta ga kwastomominsu masu rike da katin shaidar dan kasa.

Gwamnatin ta ce yanzu haka duk wani dan kasa mai rike da katin shaidar dan kasa ta NIN zai iya neman bankinsa su ba shi katin na ATM kyauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel