Shugaban INEC Ya Sanar da Ma'aikatan Hukumar Abin da ba Za Su Yarda da Shi ba

Shugaban INEC Ya Sanar da Ma'aikatan Hukumar Abin da ba Za Su Yarda da Shi ba

  • Shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikatan hukumar da su guji nuna goyon baya ga kowace jam’iyyar siyasa, su kuma kasance masu adalci da ƙwarewa
  • Hukumar ta bullo da tsarin lada da hukunci domin ƙarfafa ladabtarwa da ɗaukar alhaki a ofisoshinta na ƙananan hukumomi, jihohi da ƙasa baki ɗaya
  • Amupitan ya ce sabon tsarin albashin ma’aikatan INEC zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2027, da nufin inganta jin daɗinsu da rage yiwuwar karɓar rashawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Enugu, jihar Enugu - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya gargaɗi ma’aikatan hukumar.

Farfesa Amupitan ya gargade su kan shiga siyasar jam’iyya, inda ya buƙace su da su kasance masu tsaka-tsaki da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu.

INEC ta ja kunnen ma'aikata
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Amupitan ya yi wannan gargaɗi ne ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban 2026 yayin wata ganawa da ma’aikatan INEC na shiyyar Kudu maso Gabas, jim kaɗan bayan isarsa Enugu a ziyarar aiki.

Kara karanta wannan

An kai maganar barazana kan rayuwar Atiku gaban Shugaba Trump

Ziyarar na da nufin ganawa da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe a yankin.

INEC ba za ta lamunci nuna son kai ba

Shugaban hukumar ya ce ba za su lamunci rashin ɗa’a ko duk wani hali da ka iya raunana amincewar jama’a da tsarin zaɓe ba.

“Kada ku nuna sha’awa ga kowace jam’iyyar siyasa. Ku kasance masu tsaka-tsaki kuma masu tsayawa kan gaskiya. Ina jin cewa wasu daga cikinku na nuna sha’awa ga wasu jam’iyyun siyasa. Wannan ba daidai ba ne sam.” In ji shi.

Amupitan ya ƙara da cewa hukumar na son ma’aikatanta su kasance masu tsaka-tsaki da ƙwarewa, a maganganunsu da kuma ayyukansu.

Ya ce INEC ba za ta amince da duk wani aiki marar ƙwarewa ko wanda ya saɓa wa ƙa’idojin ɗabi’a daga ma’aikatanta ba.

Hukumar ta bullo da tsarin lada da hukunci

Amupitan ya bayyana cewa hukumar ta bullo da tsarin bayar da lada da kuma hukunta ma’aikata, wanda ya shafi ofisoshinta na ƙananan hukumomi, jihohi da kuma matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An maka INEC kara gaban kotu kan N126bn

Ya ce an samar da tsarin ne domin ƙarfafa ladabtarwa da tabbatar da cewa ma’aikata suna ɗaukar alhakin ayyukansu.

Sabon tsarin albashi zai fara aiki a 2027

Shugaban INEC ya kuma sanar da shirin sauya tsarin albashin ma’aikatan hukumar daga tsarin albashin ma’aikatan gwamnati na yau da kullum zuwa wani tsari na musamman.

A cewarsa, ana sa ran sabon tsarin zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2027. Ya bayyana cewa manufar sauyin ita ce inganta jin daɗin ma’aikata da rage yiwuwar jawo hankalin jami’an zaɓe su karɓi rashawa kafin zaɓe, yayin zaɓe ko bayan kammala shi.

“Muna son sabon tsarin albashi ne domin kada ya zama na cokin sauƙi a rinjaye ku da kuɗi kafin zaɓe, lokacin zaɓe ko bayan zaɓe.” In ji shi.
Amupitan ya ja kunnen ma'aikatan INEC
Farfesa Joash Amuoitan na jawabi a wajen taro Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

SERAP ta shigar da kara kan INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ungiyar SERAP mai ta maka Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kara a gaban kotu.

Ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin INEC da gaza bayar da cikakken bayani kan sama da Naira biliyan 126.46 da aka ware wa ayyukan zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng