Gani ga Wane: Gwaman Ya Raba Sarki da Rawani, Fadarsa kan Tsunduma Kansa a Siyasa
- Gwamnatin Ogun ta dakatar da wani Sarki a masarautar Iselu, bisa zargin shiga harkokin siyasa
- Gwamnatin ta ce matakin ya biyo bayan korafe-korafe da dama kan ayyukan basaraken, inda ta umurci a gudanar da bincike
- An umarci sarkin ya bar fadarsa, ya daina amfani da rawani da sauran kayan sarauta, an hana zuwa zaman bincike da gwamnati ta kira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Iselu, Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da Eselu na masarautar Iselu da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa.
An dakatar da Oba Akintunde Akinyemi, nan take bisa zargin shiga harkokin siyasa wanda hakan ya sabawa doka.

Source: Original
A cewar wata sanarwa da mai ba Gwamna Dapo Abiodun shawara kan harkokin yada labarai, Kayode Akinmade, ya fitar, cewar Punch.
Majalisar zartarwa ta jihar ce ta amince da dakatarwar bisa sashe na 52(1) na dokar sarakuna da masu sarauta ta Ogun ta shekarar 2021, har sai an gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa sarkin.
Sanarwar ta ce an isar da matakin ta hanyar wata wasika mai kwanan watan 20 ga Oktoba, 2026, wadda kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Ganiyu Hamzat, ya sanya wa hannu.
Wasikar ta bayyana cewa majalisar ta dauki matakin ne bayan samun korafe-korafe da dama kan halayen sarkin, musamman zargin shiga harkokin siyasa karara, wadanda wasu daga cikinsu aka ce ya wallafa a bainar jama'a.
Gwamnatin ta bayyana cewa shiga siyasar jam’iyya ya saba wa dokokin gargajiya, kuma doka ta haramta hakan.
Ta yi gargadin cewa irin wannan hali na iya rage martabar sarautar gargajiya da kuma kawo barazana ga zaman lafiya tsakanin al’ummar da ke da ra’ayoyin siyasa mabambanta.
Ta ce an dauki matakin dakatarwar ne domin tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, da kyakkyawan shugabanci a jihar Ogun, musamman a masarautar Iselu, yayin da ake gudanar da bincike kan zarge-zargen.
A matsayin wani sharadi na dakatarwar, an umarci Oba Akinyemi ya fice daga fadarsa, kuma kada ya sake shiga cikinta a tsawon lokacin da aka dakatar da shi.
Haka kuma, an umurce shi da kada ya gabatar da kansa ko ya amince da duk wani kiran da ke nuna cewa shi ne Eselu na masarautar Iselu.
Gwamnatin ta kuma haramta masa sanya ko amfani da kowane irin rawani, ko mai ado da beads ko wanda ba shi da irin wannan ado, ileke, sandar sarauta mai beads, irukere ko wasu kayan da ake dangantawa da ofishin sarki a lokacin dakatarwar.
Wasikar ta kuma umurci sarkin da ya kasance a shirye domin halartar duk wani taro ko zaman da gwamnatin jihar za ta kira domin binciken zarge-zargen da ake yi masa.
An aika kwafin wasikar ga sakataren karamar hukumar Yewa North da kwamishinan ‘yan sandan rundunar jihar Ogun domin saninsu da daukar matakin da ya dace.
Wata wasikar dakatarwar da wakilinmu ya gani ranar Talata, wadda kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Ganiyu Hamzat, ya sanya wa hannu, ta ce:
“A ‘yan kwanakin nan, majalisar zartarwa ta jihar ta samu korafe-korafe da dama dangane da ayyukanku a matsayinku na sarkin gargajiya.
“Musamman, majalisar ta samu korafe-korafe da dama kan ayyukan siyasa karara da kuke yi ko kuke umartar a yi, inda aka wallafa da dama daga cikinsu a bainar jama’a.
“Kamar yadda kuka sani, shiga siyasar jam’iyya ya saba wa dokokin gargajiya. Haka kuma, dokokin kasa sun haramta hakan, domin yana iya rage martabar sarauta tare da haddasa tabarbarewar doka da oda tsakanin talakawanku masu ra’ayoyin siyasa daban-daban."
Sarki ya ba mutane shawara kan yan siyasa
A baya, kun ji cewa Sarkin Iselu, Oba Akintunde Akinyemi, ya bukaci al’ummar Ogun su ki zaben ’yan siyasar da ba sa amsa kiransu ko sakonninsu.
Sarkin ya ce rashin sadarwa tsakanin shugabanni da jama’a na iya haifar da rashin amincewa da jita-jita.
Oba Akinyemi ya bukaci sarakuna, ’yan siyasa da masu kada kuri’a su dauki amsa kira da sakonni a matsayin muhimmin tsarin shugabanci.
Asali: Legit.ng


