Dala Ta Kara Karyewa a Kasuwar Ƴan Canji Yayin da Darajar Naira Ta Ƙaru a Najeriya

Dala Ta Kara Karyewa a Kasuwar Ƴan Canji Yayin da Darajar Naira Ta Ƙaru a Najeriya

  • Kuɗin Najeriya watau Naira na ƙara daraja kan Dalar Amurka a kasuwar bayan fage ta ƴan canji ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, 2024
  • Rahoto ya nuna cewa Dala ta kara karyewa ta dawo N1,150 a kasuwar ƴan canji jim kaɗan bayan CBN ya ƙara daukar mataki
  • Babban bankin ya fara sayar da Daloli ga ƴan canji karo na uku kan farashi mai sauki duk a wani yunkuri na farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, 2024, Naira ta ƙara daraja zuwa N1,150 kan kowane Dalar Amurka ɗaya a kasuwar musayar kuɗi ta ƴan canji (FX).

Ƴan canji waɗanda ake kira da BDC masu tafiyar da kasuwancin musayar kuɗi suna sayen Dala ɗaya kan N1,110 kuma su sayar wa kwastomomi a N1,150.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya caccaki dattawan Arewa kan kalaman da suka yi game da Bola Tinubu

Naira da Dala.
Naira ta kara farfadowa a kasuwar yan canji Hoto: Central Bank
Asali: Getty Images

Yan kasuwar canjin sun riƙa sanya ribar N40 kan yadda suka sayi kowace Dala ɗaya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naira ta kara daraja da kashi 0.86 cikin 100 daga N1,160 da aka yi musaya a ranar 11 ga Afrilu, 2024, rahoton Leadership.

Har ila yau, FMDQ Exchange, wani shafi mai kula da harkokin musayar kudaden waje (FX) a Najeriya, ya ce Naira ta kara daraja da kashi 7.16% ko kuma N88.23, inda ta koma N1,142.38/1$ daga N1,230.61/1$.

CBN ya kara ɗaukar mataki

Karin darajar Naira na zuwa ne kwanaki kadan bayan da babban bankin Najeriya watau CBN, a karo na uku, ya sayar da Daloli ga ƴan canji kan farashi mai sauƙi.

Babban bankin ya fara sayar da Dalolin Amurka ga ƴan canji BDC a kan farashin N1,101/1$ a ranar 8 ga Afrilu.

Kara karanta wannan

Cikin masu boye Dala zai tsure, an yi hasashen Naira za ta cigaba da tashi a 2024

Har ila yau, a wannan rana, CBN ya umurci dukkan bankunan da su dakatar da yin amfani da kowane irin kuɗin waje yayin ba da lamuni a Naira.

Kamfanin canji na Goldman Sachs Group Inc. ya ce Naira na iya farfaɗowa zuwa ƙasa da N1,000 kan kowace Dala.

Kotu ta bada belin Emefiele

A wani rahoton na daban Wata kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele a kan N50m.

Mai shari’a Rahman Oshodi ya ce Emefiele na da bukatar mutane biyu da za su tsaya masa kuma dole su kasance masu biyan haraji ga Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel