A Karon Farko Cikin Kwanaki, Naira Ta Ci Karo da Matsala, Ta Tashi da 1.3% a Kasuwa

A Karon Farko Cikin Kwanaki, Naira Ta Ci Karo da Matsala, Ta Tashi da 1.3% a Kasuwa

  • A karon farko tun ranar 20 ga watan Maris, darajar naira ta fado kasa kan N1, 169 a kasuwannin 'yan canji a Najeriya
  • A 'yan kwanakin nan darajar naira na kara tashi wanda ya saka tsammani a zukatan 'yan Najeriya kan saukowar farashin kaya
  • Hukumar kula da cinikayyar kudi (NAFEM) ta bayyana cewa faduwar naira ta samu da kaso 1.38 idan aka kwantanta da N1,159

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Darajar naira ta sake faduwa a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu a kasuwannin 'yan canji.

A jiya ana siyar da dala kan N1,169 a kasuwanni idan aka kwatanta da ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu kan N1,154.

Kara karanta wannan

Charterhouse Lagos: makarantar firamaren da ake biyan naira miliyan 42 a Shekara

Darajar naira ta sake faduwa a kasuwannin 'yan canji
Hukumar NAFEM ta bayyana faduwar naira a kasuwa da kaso 1.38. Hoto: Central Bank of Nigeria, CBN.
Asali: UGC

Yaushe naira ta fado a kasuwa?

Hukumar kula da cinikayyar kudi ta NAFEM ta tabbatar da cewa naira ta fadi da kaso 1.38, cewar rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan faduwar naira shi ne karon farko tun a ranar 20 ga watan Maris lokacin da dala ke N1,500.

Wannan na zuwa ne bayan Babban Bankin Najeriya, CBN ya musanta siyar da dala ga 'yan kasuwa kan N1,500, cewar Newstral.

Ana hasashen kaya sun fara sauki

Har ila yau, Farfadowar darajar naira a kan dala da sauran kudaden duniya ya jawo faduwar farashin wasu kayayyaki a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai habaka yayin da farashin kayayyaki zai ci gaba da faduwa idan naira ta ci gaba da yin daraja.

Sai dai duk da faduwar dala a kasuwanni amma 'yan Najeriya ke kokawa kan yadda farashin abinci ya tsaya ba tare da yin kasa ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin tarayya ta fara bayar da tallafin N50,000 ga mutanen Najeriya

An karya farashin dala a Najeriya

A baya, kun ji cewa Ƙungiyar ƴan canji na kasuwar bayan fagen (ABCON) ta bayyana cewa ƴan kasuwar musayar kuɗin sun fara sayen Dalar Amurka kan N980/1$.

ABCON ta kuma bayyana cewa ƴan canjin suna sayar da Dalar kan N1,020/$ ga kwastomomi bayan sun saya a N980/$ watau suna ɗora ribar N40 ne kacal.

Shugaban ƙungiyar ABCON, Aminu Gwadebe, ne ya tabbatar da wannan ci gaban yayin hira da 'yan jaridu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel