Hatsarin Mota Ya Ritsa da Shugaban Majalisa, an Ji Halin da Yake ciki

Hatsarin Mota Ya Ritsa da Shugaban Majalisa, an Ji Halin da Yake ciki

  • Hatsarin mota ya ritsa da tawagar ayarin motocin shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas
  • Kakakin ya kuɓuta ba tare da rauni ba, yayin da babu wanda ya rasa ransa ko samun munanan raunuka a hatsarin
  • Hadarin ya faru ne yayin da ayarin ke dawowa Bauchi bayan ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Burra, Hon. Ibrahim Tanko Burra

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Bauchi – Ayarin motocin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman (Dangaladiman Ningi), ya yi hatsarin mota a daren Litinin, inda motoci biyu suka kauce daga kan hanya, amma babu wanda ya rasa ransa a lamarin.

An tabbatar da cewa Kakakin ya kuɓuta ba tare da samun rauni ba, yayin da babu rahoton wani babban rauni da aka samu sakamakon hatsarin.

Kara karanta wannan

Tinubu zai fara karɓar harajin 25% daga kuɗaɗen shigan ƴan Najeriya?

Shugaban majalisar dokokin Bauchi ya yi hatsari
Abubakar Y Suleiman yayin zaman majalisar dokokin jihar Bauchi Hoto: Mukhtar Garba Kobi
Source: Facebook

Kakakin majalisar Bauchi ya tsira

Mukhtar Garba Kobi, mai taimaka wa Kakakin ta fuskar yaɗa labarai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, inda ya tabbatar wa jama'a cewa motar da Kakakin ke ciki ba ta yi hatsarin ba.

Sanarwar ta ce:

"Cikin cikakken miƙa wuya ga ƙaddarar Allah Maɗaukakin Sarki, muna sanar da jama'a cikin alhini cewa ayarin motocin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman (Dangaladiman Ningi), ya yi hatsarin mota, inda motoci biyu suka kauce daga kan babbar hanya.”

Kobi ya bayyana cewa an kai mutanen da ke cikin motocin da hatsarin ya shafa asibiti domin duba lafiyarsu, kuma daga bisani sun koma gidajensu.

Ya kuma nuna godiya ga mutanen da suka taimaka wa waɗanda hatsarin ya rutsa da su nan take.

“Muna miƙa godiyarmu ta musamman ga duk waɗanda suka ba wa waɗanda hatsarin ya shafa taimako cikin gaggawa.” In ji shi.

Kara karanta wannan

"Kai ne Masar," Atiku ya maida martani bayan Tinubu ya yi misali da tarihin Annabi Musa AS

Haka kuma, mai taimaka wa Kakakin ya isar da godiyar Kakakin da Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ga mazauna Burra, Ningi da sauran sassan jihar bisa addu'o'i, goyon baya da nuna haɗin kai da suka yi a wannan lokaci.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“A madadin Kakakin Majalisar da Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, muna godiya ga al'ummar kirki ta Burra, Ningi da Jihar Bauchi baki ɗaya bisa addu'o'i, goyon baya da haɗin kai da suka nuna mana a wannan lokaci na jarabawa.”

An bayyana hatsarin a matsayin kaddara

Kobi ya bayyana hatsarin a matsayin wani al'amari da ya faru bisa ƙaddara, yana mai cewa Kakakin da tawagarsa sun karɓi abin da ya faru a matsayin ƙaddarar Allah Maɗaukakin Sarki.

Duk da hatsarin, Suleiman ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da sauke nauyin da ke kansa na majalisa, tare da tallafa wa 'yan takarar jam'iyyar Allied People’s Movement (APM) gabanin zaɓukan da ke tafe.

Kakakin ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka da oda, tare da yawaita addu'o'i.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya ci gaba da kare al'umma, tare da gaggauta warkar da waɗanda suka samu raunuka a hatsarin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi misali da Annabi Musa kan batun dawo da tallafin fetur

Kakakin majalisar dokokin Bauchi ya yi hatsari
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban Miyetti Allah ya rasu a hatsarin mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kungiyar Miyetti Allah, MACBAN na Babban Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Ardo Wokili Madugu, ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a jihar Neja.

Hatsarin ya afku ne a hanyar Lambata-Izom, inda wata tirela ta faɗa cikin wani babban rami, sannan ta faɗa kan motar da Madugu ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng