Murna Yayin da Dala Ta Karye Zuwa Ƙasa da N1,000 a Najeriya, Hadimin Buhari Ya Magantu

Murna Yayin da Dala Ta Karye Zuwa Ƙasa da N1,000 a Najeriya, Hadimin Buhari Ya Magantu

  • Bashir Ahmad ya ce ya samu sahihin bayanin cewa ana musayar Dala kan farashi ƙasa da N1,000 a wurin wasu ƴan canji a Najeriya
  • Ahmad, tsohon hadimin shugaban ƙasa a gwamnatin Muhammadu Buhari ya nuna kwarin guiwar cewa Naira za ta ci gaba da tashi
  • Legit Hausa ta tattaro muku cewa Naira na ci gaba da farfaɗowa kan Dalar Amurka tun farkon watan Afrilu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce yanzu haka darajar Dalar Amurka ta karye zuwa ƙasa da N1000.

Tsohon hadimin shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa ya samu sahihan bayanai cewa farashin Dala ya faɗo zuwa ƙasa da N1000 a wurin wasu ƴan kasuwar bayan fage (BDCs).

Kara karanta wannan

Kano: 'Yaran' Kwankwaso sun shiga gagarumar matsala kan dakatar da Ganduje

Naira ta farfado a kasuwa.
Bashir Ahmad ya tabbatar da cewa Dala ta kawo ƙasa da N1000 Hoto: Maskot, Effi
Asali: Getty Images

Hakan na kunshe ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter da daren ranar Lahadi, inda ya yaba da matakan da babban banki CBN ya ɗauƙa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir Ahmad ya yabawa CBN

Tsohon hadimin Buhari ya ce babu shakka matakan da CBN ya ɗauka suna aiki sosai kuma ga dukkan alamu Naira za ta ci gaba kai Dala ƙasa a kasuwar musayar kuɗi.

Ahmad ya ce:

"Na samu tabbacin cewa yanzu haka ana canjin Dalar Amurka kan kuɗi ƙasa da N1,000 a wurin wasu ƴan kasuwar canji. Matakan da CBN ke ɗauka na farfaɗo da kuɗin Najeriya suna aiki. Naira za ta ci gaba da tasowa."

Ƴan Najeriya sun yi magana

Bayan wannan ikirari na Bashi Ahmad, an samu wasu ƴan Najeriya da suka bayyana ra'ayoyinsu kan wannan ci gaban.

Kara karanta wannan

Muna buƙatar bishiya 1 tsakanin gidaje 5 don yaƙar dumamar yanayi inji Anka

@OlabisiLaw ya ce:

"Na yi canji kan N1070 jiya (Asabar 13 ga watan Afrilu), muna fatan hakan ya ɗore domin wannan ci gaba ne mai kyau."

Raji AbdulJelil ya ce:

"Ina farin ciki da zuwan Cardoso (gwamnan CBN), ya ɗauko babban aiki mai kyau."

Ebele Obi ya ce:

"Za ta ƙara karyewa zuwa N650, wannan ne hasashen da ake ma Dalar Amurka yanzu haka."

CBN ya kara sayar da Dala

A wani rahoton kuma Babban bankin Nijeriya (CBN) ya kuma ba 'yan canji $10,000 a kan farashin N1,101/$ bayan da ya kafa masu sharadi na siyarwa.

Bankin ya gargadi 'yan canjin cewa kada su siyar da $1 ta haura ribar kaso 1.5% na yadda ya ba su ita a farashin sari (N1,269/$).

Asali: Legit.ng

Online view pixel