'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'in Tsaro tare da Sace Hamshakin Attajiri a Plateau

'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'in Tsaro tare da Sace Hamshakin Attajiri a Plateau

  • Wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC tare da yin garkuwa da wani ɗan kasuwa a Plateau
  • Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare ranar Litinin, bayan maharan sun sace ɗan kasuwar da ke sana’ar mai, siminti da takin zamani
  • Al’ummar yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Filato da su ƙara tsaurara matakan tsaro tare da tabbatar da kuɓutar ɗan kasuwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC), tare da yin garkuwa da wani ɗan kasuwa a garin Pushit da ke ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na daren ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban 2026 bayan maharan sun sace ɗan kasuwar.

Kara karanta wannan

2027: Shugaban INEC ya sanar da ma'aikatan hukumar abin da ba za su yarda da shi ba

An kashe jami'in NSCDC a Plateau
Jami'in hukumar NSCDC a bakin aiki Hoto: @OfficialNSCDC
Source: Twitter

Daily Trust ta ce mazauna yankin da kuma ’yan uwan mamacin sun bayyana cewa bayan ’yan bindigar sun yi garkuwa da ɗan kasuwar, sai suka hango jami’in NSCDC yana kan hanyarsa ta zuwa wani shago domin sayen katin waya, inda suka buɗe masa wuta.

'Yan bindiga sun kashe jami'in NSCDC

Sun ƙara da cewa maharan sun yi zaton jami’in, wanda yake sanye da kayan farar hula, ya nufo su ne domin hana su sace ɗan kasuwar, ba tare da sanin cewa yana tafiya ne zuwa wani wuri na daban ba.

Wani mazaunin yankin mai suna Lawrence Tabitha ya shaida wa manema labarai cewa mamacin, wanda yake muƙaddashin babban sifeton NSCDC, an harbe shi ne a kusa da gidansa yayin da yake tuƙa babur.

“’Yan bindigar sun fara yin garkuwa da wani ɗan kasuwa da ke sana’ar sayar da mai, siminti da takin zamani. Maharan sun buɗe wa jami’in NSCDC wuta ne bayan hasken fitilar babur ɗinsa ya fallasa motsinsu yayin da suke tserewa daga yankin tare da mutumin da suka sace.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An maka INEC kara gaban kotu kan N126bn

Mutane sun shiga fargaba

Ya ƙara da cewa lamarin ya ƙara jefa mazauna Pushit da sauran al’ummomin da ke kewaye da yankin cikin fargaba kan matsalar tsaro, duk da matakan da aka ɗauka domin dakile hare-hare.

Tabitha ya buƙaci hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Filato da su ɗauki matakan gaggawa domin ƙarfafa tsaro a gundumar Pushit tare da tabbatar da sakin ɗan kasuwar cikin ƙoshin lafiya.

Ya ce mazauna yankin sun fi damuwa ne saboda yawan hare-haren da ake kai wa al’ummomin da ke gundumar, ciki har da Vodni, Sabon Gari da Nchiya.

Da aka tuntubi kakakin rundunar NSCDC ta jihar Filato, ASP AR Rimvyok, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “Gaskiya ne.”

'Yan bindiga sun yi barna a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe jagoran 'yan bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa mayakan da ke biyayya ga fitaccen jagoran ’yan bindiga, Aleru, sun kashe wani jagoran ’yan bindiga da ake kira Kachallah Dogo Baldu.

An kashe Dogo Baldu ne yayin arangama tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga masu hamayya da juna a gabashin Mada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng