Tashin Farashin Dala: Kokarin da CBN Yake Yi Na Daidaita Naira a Kasuwar Canji

Tashin Farashin Dala: Kokarin da CBN Yake Yi Na Daidaita Naira a Kasuwar Canji

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce kada hawa da saukar darajar Naira a kasuwar hada-hada (FX) ya ba mutane tsoro, na lokaci ne kawai
  • Yemi Cardoso, gwamnan CBN wanda ya bayyana hakan ya ce yana yin duk mai yiwuwa domin ganin an samu daidaiton kudin
  • Har ila yau, Cardoso ya ce Najeriya ta samu amsa mai kyau daga masu saka hannun jari na kasashen waje (FPI) kuma adadin ya karu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Washington DC, Amurka - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce yana yin duk mai yiwuwa domin ganin an samu daidaiton farashin Naira a kasuwar hada-hadar kudade (FX).

Babban bankin Najeriya ya yi magana kan hawa da saukar farashin Naira
Gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya ce bankin na yin duk mai yiwuwa domin daidaita darajar Naira. Hoto: @DrYemiCardoso
Asali: UGC

Yemi Cardoso, gwamnan CBN ne ya bayyana haka a ranar 20 ga watan Afrilu a zantawarsa da manema labarai a wajen taron shekara shekara na asusun lamuni na duniya (IMF) da Bankin Duniya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu na shirin karbar sabon bashin Dala biliyan 2.2 daga Bankin Duniya

CBN na kokarin daidaita Naira

Ya ce bankin wanda ke kula da hada-hadar kudi na kasar yana kuma kokarin ganin an samu farashi mai kyau da za a rika musayar Naira, jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Magana ta gaskiya za a samu hawa da saukar farashi da kuma koma baya amma ko a jiya kun ruwaitoyadda Naira ta fara farfadowa a cikin dare.
“Don haka ina ganin abin da ya fi muhimmanci a ce a nan shi ne muna yin duk mai yiwuwa don ganin mun samu daidaiton farashin Naira a kasuwar canji."

- A cewar Cardoso.

CBN za ta nunka hada-hadar kudade

Jaridar Vanguard ta rahoto gwamnan babban bankin ya ce kudaden kasar za su ci gaba da kara yin daraja a kan kudaden kasashen waje.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta fara ƙera motoci gadan-gadan, gwamnatin tarayya ta yi bayani

Dangane da kuɗaɗen da ake kai wa ƙasashen waje, Cardoso ya ce burin bankin shi ne ya ninka kuɗin da ake hada-hadar su a yanzu.

A cewar gwamnan na CBN, ana iya ganin abin da ake son cimmawa kamar yayi yawa, amma ya bayyana kwarin gwiwar cewa kasar za ta iya cimma hakan.

CBN ta samu karin masu saka jari

Har ila yau, Cardoso ya ce kasar za ta ci gaba da sanya masu zuba jari a tattaunawar da ta shafi inda aka kwana kan sauye-sauyen da bankin ya aiwatar ya zuwa yanzu.

Ya kuma ce an samu amsa mai kyau daga masu saka hannun jari na kasashen waje (FPI), a cewar rahoton talabijin na Channels.

"Amsar da muka samu daga masu zuba jari na kasashen waje abun jin dadi ne, adadin yana ta karuwa kuma muna fatan za mu kara jawo ra'ayin su har mu samu abin damuke so."

Kara karanta wannan

A karon farko cikin kwanaki, naira ta ci karo da matsala, ta tashi da 1.3% a kasuwa

- A cewar gwamnan CBN.

Najeriya za ta karbi bashin $2.2bn

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito ministan kudi, Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta karbi bashin $2.2bn daga Bankin Duniya.

Ministan wanda ya bayyana hakan a wajen taron shekara shekara na asusun lamuni na duniya (IMF) da Bankin Duniya ya ce babu kudin ruwa mai yawa a kan bashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel