Abin da Tinubu Ya Cewa ‘Dansa Seyi da Ya Gana da ‘Yan City Boy a Aso Rock
- Bola hmed Tinubu ya yaba wa dansa Seyi Tinubu kan ayyukansa a kungiyar City Boy Movement a Najeriya
- Mai girma Shugaban kasar ya ce ‘dansa yana bin sawun ne, kuma bai neman wani mukami ko ofishi a gwamnati
- Tinubu ya umurce Seyi da ya kara kwazo har ya zama misali ga ‘yan baya har yana cewa zai yi takara bayan shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa dansa, Seyi Tinubu, bisa ayyukan da yake yi na tallar gwamnatinsa.
Seyi Tinubu yana kokari ne karkashin kungiyar City Boy Movement ta matasa da ya kafa mai jama’a a birnin Abuja da jihohi 36.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya hadu da kungiyar City Boy
Bola Tinubu ya bukace shi da ya kara kokari, ya himmatu wajen yi wa kasa hidima kamar yadda Punch ta kawo rahoto.

Kara karanta wannan
Kamfen 2027: Dalilin da ya sa Shugaba Tinubu ya zaɓi Kano da wasu jihohi 11 a Najeriya
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wani taro da kungiyar ta shirya a fadar shugaban kasa a birnin Abuja.
Shugaban kasar ya ce yana alfahari da yadda Seyi ke hada matasa wuri guda, duk da cewa bai nemi wani mukamin siyasa ba.
Shugaban na Najeriya yana so Seyi Tinubu ya cigaba da zama abin koyi ga masu tasowa.
“Na samu wasu kiraye-kiraye a makonnin baya, inda ake tambayata takarar me Seyi yake yi. Zai yi takara bayan mahaifinsa ne,”
- in ji Tinubu
Abin da ya burge Tinubu game da Seyi
An ya yabi Seyi da abokan aikinsa bisa yadda suke amfani da lokacinsu wajen hulda da matasa da sauraron matsalolinsu.
Tinubu ya ce matakin da ‘dansa, Seyi ya dauka na shiga cikin matasa da sauraron ra'ayoyinsu abin a yaba masa ne.
Ya kara da cewa yana alfahari da su saboda ba su nemi mukami ko wata kujera a gwamnatinsa ba shekaru uku da shiga ofis.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda Buhari ya nuna akwai matsala idan Tinubu ya karbi mulki a 2023
Tashar TVC ta ce Kashim Shettima ya halarci zaman da aka yi a Aso Rock a yammacin na Litinin.
Kiran da shugaban kasa ya yi wa 'dansa
Sai dai Mai girma Tinubu ya gargadi dansa da kada ya sake ya ci burki saboda ganin nasarorin da ya samu zuwa yanzu.
Shugaban kasar da yake fuskantar zabe ya bukace shi da ya kara kokari tare da himmatuwa wajen yi wa Najeriya hidima.
“Zan gaya maka abin da kowane uba ke gaya wa dansa. Yanzu ka fara. Ka kara kokari, ka dage, ka yi hidima da himma, sannan ka zama abin koyi da yaranka da jikokina za su yi alfahari da shi,” in ji shi.
Tsohon gwamnan na Legas ya kara da cewa ya kamata 'yan Najeriya su fahimci cewa yi wa kasa hidima babbar daraja ce.
An yi karya da sunan ministan Tinubu
Ana ta cin karo da karyayyaki a shafukan sada zumunta musamman saboda manufar siyasa kamar yadda muka bayyana a wani rahoto.
Zancen dawo da takarar Isa Pantami da cewa Adebayo Adelabu yana yakar APC a Oyo suna cikin labaran kanzon kurege da suka yi ta yawo.
Wani labarin karya da ya shahara ya fito dangane da Atiku Abubakar da mabiya shi’a, ana cewa ya ce zai yake su idan ya samu mulki.
Asali: Legit.ng
