Kwankwaso Ya Fito Ya Yi Maganar Dalilin da Ya Sa Atiku ba Zai Iya Kifar da Tinubu ba

Kwankwaso Ya Fito Ya Yi Maganar Dalilin da Ya Sa Atiku ba Zai Iya Kifar da Tinubu ba

  • Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi zargin cewa Atiku Abubakar ba shi da irin tasirin siyasa da marigayi Muhammadu Buhari ya samu a Arewacin Najeriya
  • Jigon na APC ɗin ya ce masu zaɓe a Arewa sun fi mayar da hankali kan ayyukan shugabanci da ci gaba fiye da ƙabilanci ko addini
  • Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Bola Tinubu zai ci gaba da kasancewa ɗan takara mai ƙarfi a Arewa a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kano, Dr Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi magana kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce Atiku ba shi da tasirin siyasa da goyon bayan Arewa irin na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari da zai iya barazana ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Sanata Tambuwal na shirin ficewa daga ADC zuwa APC? An ji yadda zancen yake

Kwankwaso ya ce Atiku ba zai kayar da Tinubu ba
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya rabawa ’yan jarida, Kwankwaso ya ce yanayin siyasar Arewacin Najeriya ya sauya, cewar rahoton jaridar Leadership.

Ya bayyana cewa Atiku ba zai iya dogaro da ra’ayoyin ƙabila da yanki domin samun goyon bayan masu zaɓe Hausawa da Fulani kamar yadda ake tsammani ba.

Kwankwaso ya kwatanta Atiku da Buhari

Jigon na APC ya ce Buhari ya samu karɓuwa sosai a Arewacin Najeriya, amma a cewarsa, Atiku bai iya samun irin wannan karɓuwa ba duk da tsawon shekarun da ya shafe yana siyasa a matakin ƙasa.

“Atiku ba Buhari ba ne. Ba shi da girma, matsayi da karɓuwar da marigayi shugaban Najeriya yake da su da za su ba shi damar zama barazana ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.” In ji shi.

An ƙalubalanci Atiku kan ayyukansa a lokacin mulki

Kwankwaso ya kuma yi tambaya kan irin nasarorin da Atiku ya samu a lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa na tsawon shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Ya ƙalubalanci Atiku da ya bayyana ayyukan ci gaban da aka gudanar a lokacin mulkinsa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen nuna abin da zai iya samar wa ’yan Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.

A cewarsa, masu zaɓe a Arewa na ƙara mayar da hankali kan ingancin shugabanci, ayyukan ci gaba da manufofin da za su inganta rayuwarsu, maimakon la’akari da ƙabila ko addini kawai, jaridar Tribune ta kawo labarin.

“Arewa ta wuce tunanin da ya dogara da tsofaffin ra’ayoyi, kuma dogaro da katin ƙabilanci da addini tabbas ba zai taimake shi ba.” In ji shi.

Batun tasirin Atiku a tsakanin masu zaɓe

Jigon na APC ya kuma yi zargin cewa abokan siyasar Atiku sun san cewa tasirinsa a tsakanin masu zaɓe Hausawa da Fulani ba shi da yawa.

Ya yi ikirarin cewa wannan ne ya sa aka fara ƙoƙarin raunana ko wargaza jam’iyyar NDC. Sai dai sanarwar ba ta kawo hujjoji masu zaman kansu da za su tabbatar da wannan zargi ba.

Kwankwaso ya yi magana kan Atiku
Jigon APC a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso
Source: Twitter

Kwankwaso ya yi wa ADC martani mai zafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani mai zafi ga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kan zarge-zargenta.

Kwankwaso ya ce NDC ba za ta janye wa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, takara domin goyon bayan jam’iyyar ADC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng