An Ƙara Karya Dala a Najeriya, ABCON Ta Faɗi Sabon Farashin Saye da Sayarwa

An Ƙara Karya Dala a Najeriya, ABCON Ta Faɗi Sabon Farashin Saye da Sayarwa

  • Alamun sauƙi na ta kara bayyana yayin da ƴan kasuwar musayar kuɗi suka ƙara karya farashin Dalar Amurka zuwa ƙasa da Naira dubu ɗaya
  • Shugaban ƙungiyar ƴan canji (ABCON), Aminu Gwadabe, ya bayyana cewa yanzu haka suna sayen Dala N980 su sayar da ita kan N1040
  • Ya yabawa gwamnatin tarayyar Najeriya da babban bankin CBN bisa matakan da suka ɗauka wanda ya dawo da martabar Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙungiyar ƴan canji na kasuwar bayan fagen (ABCON) ta bayyana cewa ƴan kasuwar musayar kuɗin sun fara sayen Dalar Amurka kan N980/1$.

ABCON ta kuma bayyana cewa ƴan canjin suna sayar da Dalar kan N1,020/$ ga kwastomomi bayan sun saya a N980/$ watau suna ɗora ribar N40 ne kacal.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya ragu a wasu gidajen mai yayin da Dala ta ƙara karyewa a Najeriya

Naira da Dala.
Yan canji sun fara sayen Dalar Amurka kan N980 a Najeriya Hoto: @Centralbank
Asali: Getty Images

Naira tana hawa kan Dala a BDC

Shugaban ƙungiyar ABCON, Aminu Gwadebe, ne ya tabbatar da wannan ci gaban yayin da ya bayyana a cikin wani shirin kasuwanci na tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ƙara da cewa Naira na ci gaba da ƙara daraja a kan Dalar Amurka fiye da yadda masu hasashe suka yi tsammani.

Dala: ABCON ta yabawa CBN da Gwamnati

Gwadebe ya yabawa gwamnatin tarayya karƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da babban bankin Najeriya (CBN) bisa kokarin da suke yi har zuwa yanzu.

Ya ce wannan shi ne karo na farko a shekaru 15 da farashin Dala a kasuwar bayan fage ya fi arha fiye da farashin da ake musaya a kasuwar gwamnati.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Gwadabe ya ce yanzu hankalin kowa a kwance yake a kasuwar saboda raɗe-raɗin da ke lalata lamarin babu shi a yanzu.

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutum 45 sun rasa rayukansu sakamakon barkewar sabuwar cuta

Shugaban ABCON ya ce:

"A wurinmu muna sayen kowace Dala ɗaya a kan N980 kuma muna sayarwa a kan N1,020 yanzu haka. An samu ƙwarin guiwa."
"Yanzu haka muna da tarin kudaden waje da ‘yan kasashen waje ke shigowa da su saboda dimbin manufofin da CBN ya ɓullo da su waɗanda suka daidaita yada kuɗin za su riƙa shigowa."

Ƙimar Dalar Amurka ta ƙara faɗuwa

A baya mun kawo muku rahoton cewa Bashir Ahmad ya ce ya samu sahihin bayanin cewa ana musayar Dala kan farashi ƙasa da N1,000 a wurin wasu ƴan canji a Najeriya

Ahmad, tsohon hadimin shugaban ƙasa a gwamnatin Muhammadu Buhari ya nuna kwarin guiwar cewa Naira za ta ci gaba da tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel